Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yabon gwani ya zama dole
2020-09-08 17:30:54        cri

Da safiyar yau Talata 8 ga watan Satumba ne, shugaban kasar Sin, kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar, Xi Jinping, ya gabatar da lambar yabo ta kasa, wadda ke zaman karramawa ta koli ta kasar, ga wasu mutane hudu da suka taka rawar gani a yakin da kasar ta yi da cutar numfashi ta COVID 19.

Sanin kowa ne cewa, duk da bincike ya nuna samun cutar COVID-19 a wasu kasashen yammacin duniya cikin shekarar 2019, kasar Sin ce ta fara sanar da bullarta a hukumance a karshen bara, inda aka same ta a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar.

Bisa namijin kokarin gwamnatin kasar da kwararru da sauran al'umma, kasar ta yi iyakacin kokarin dakile bazuwar cutar, duk da cewa wasu kasashen duniya ba su dauki batun da muhimmmanci ba, ita dai a nata bangaren, ta yi nasarar dakile cutar a tsakanin al'ummarta da wuri, haka kuma ta kula da wadanda suka kamu.

Lallai matakan kasar Sin sun cancanci yabo, haka zalika jaruman da suka yi yaki a fagen daga ba da makami ba. Duk da cewa wannan cuta tana da hadarin gaske, inda take yaduwa cikin sauri tare da kai wa ga kisa, kwararru har ma da sauran al'ummar kasar Sin sun hada kai tare da sadaukar da lokacinsu da rayuwarsu ta yau da kullum, wajen kokarin ganin sun yaki da cutar cikin hadin kai. Sakamakon haka, a ganina, yabon gwani ya zama dole, al'ummar kasar Sin sun sake samun gagarumar nasara a yakin da bil-Adama ke yi da cututtuka, cikin hadin kai da kishin kasa.

A jawabin da ya gabatar yayin taron da ya gudana a yau Talata a birnin Beijing, shugaba Xi ya ce, kasar Sin ta sake taka rawar gani a yakin da bil-Adama ke yi da cututtuka. Shugaban ya kuma bayyana cewa, kokarin kasar na yaki da annobar COVID-19, ya nuna muhimmancin rayukan jama'a, da kishin 'yan kasa baki daya da sadaukarwa, da mutunta shawarwarin kimiya da mutunta daukacin bil-Adama.

Hakika, ba za a taba raba nasarar da kasar Sin ta samu wajen yakar cutar da kishi da hadin kai irin na al'ummarta ba. Yayin da kasar ta shimfida matakan yaki da cutar, dukkannin al'ummarta sun zage damtse wajen bada tasu gudunmawa a bangaren da suka fi kwarewa, don ganin sun aiwatar da matakai cikin nasara.

A cewar shugaban, miliyoyin jami'an lafiya ne suka kasance gaba-gaba wajen yaki da cutar, kuma kusan rabi daga cikinsu matasa ne da ba su haura shekaru 31 ba. Shakka babu, wannan ya nuna irin karsashi da sadaukarwa dake cikin zukatan Sinawa, wanda ba tsakanin wadanda suka manyanta kadai ake samu ba, har ma da matasa masu jini a jika. Sannan ya nuna karfi da kudurin al'ummar kasar na ganin sun shawo kan kalubalen dake gabansu ba tare da neman taimako ba.

Wannna karramawa ta yau, ta nuna cewa gwamnati na sane da irin gudunmawa da sadaukarwa da al'ummarta ke yi wajen gina kasa da shawo kan matsaloli bisa karfinsu. Haka zalika, za ta zama karin kwarin gwiwa ga al'ummar, wajen sake himmantuwa dangane da batutuwan da suka shafi kasarsu. Baya ga haka za ta karfafawa matasa da sauran zuri'a masu tasowa gwiwar bada tasu irin taimako.

A duk lokacin da aka yi gwaninta, to yana da kyau a yaba. Kamar yadda bahaushe kan ce, yaba kyauta tukwici. A nan, gwamnatin kasar Sin ta bada tukwicin gudunmawar da al'ummarta suka bayar, duk da cewa, aikin da suka yi, hakki ne da ya rataya a kan kowane dan kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China