Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun nuna himma wajen halartar taron bajekolin cinikin hidimomi
2020-09-09 10:47:08        cri


Aikin yawon shakatawa daya ne daga cikin bangarorin samar da hidimomi, wanda kuma ya kasance gishikin tattalin arzikin wasu kasashen dake nahiyar Afirka. Sai da annobar COVID-19 ta haifar da illa sosai ga wannan bangare, lamarin da ya sa wasu kasashen Afirka ke nuna himma wajen halartar taron bajekolin cinikin hidimomin dake gudana a kasar Sin, don janyo karin masu sha'awar yawon shakatawa na kasar Sin, wadanda za su ziyarci kasashen.

A yayin taron bajekolin cinikin hidimomi dake gudana a nan birnin Beijing, akwai rumfunan kasashen Afirka daban daban. Inda a rumfar kasar Angola, wani ma'aikaci mai suna Jose Andrade ya gaya wa wakilinmu cewa, "Mutane da yawa sun zo, an raba musu littattafan bayaninmu. Na yi ta magana har muryata ta dushe."

A shekarun baya, kasar Angola na kokarin raya harkoki masu alaka da al'adu da yawon shakatawa, don neman daidaita tsarin tattalin arzikin kasar, wanda ke dogaro kacokam kan harkar hakar danyen mai. Saboda haka, ana son yin amfani da wannan dama ta ciniki mai alaka da aikin samar da hidimomi, domin yayata albarkatun yawon shakatawa na kasar Angola. A cewar jakadan kasar Angola dake kasar Sin, Joao Salvador Neto, yadda ake halartar wannan taro zai sa jama'a da dama su kara sanin kasarsa. Ya ce, "Muna nuna al'adu da albarkatunmu na yawon shakatawa, wadanda suka sha bamban da harkar sarrafa danyen mai. Wannan taro, wata dama ce mai kyau a gare mu, ta yadda za mu nuna abubuwan da muke da su ga jama'ar kasar Sin."

Alkaluman da majalisar kula da sana'ar yawon shakatawa ta duniya ta gabatar sun nuna cewa, a shekarar 2019 kadai, harkokin yawon shakatawa sun sa kasashen Afirka samun kudin da ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 170, da miliyoyin guraben aikin yi. Sai dai bayan barkewar cutar COVID-19, bangaren yawon shakatawa a wasu kasashen Afirka ya gamu da matsala sosai, ciki har da kasar Botswana dake kudancin nahiyar Afirka. Saboda haka, a yayin taron bajekolin hidimomi, kasar ita ma tana kokarin tallata albarkatunsu na yawon shakatawa. Emmanuel Pheko, wani jami'in dake aiki a gidan jakadancin kasar Botswana a kasar Sin, ya ce, (3)

"Annobar COVID-19 ta takaita harkokin yawon shakatawa a tsakanin kasashe, hakan ya sa kudin da kasar Botswana take samu a wannan bangare ya ragu sosai a bana. Mun san Sinawa na son zuwa yawon shakatawa a kasashe daban daban, don haka muna fatan janyo hankali wasunsu don su zo yawon bude ido a Botswana."

A nata bangare, kasar Rwanda ita ma tana dogaro kan sha'anin yawon shakatawa sosai. A farkon watan Agustan bana, kasar ta samu takardar shaida daga majalisar kula da harkokin yawon shakatawa ta duniya, cewa yin yawon shakatawa a kasar yana da tsaro, ba za a fuskanci annoba ba. A wajen taron bajekolin hidimomi, Samuel Abikunda, mai ba da shawara ga jakadan kasar Rwanda a kasar Sin, a fannin aikin kasuwanci, ya yi amfani da yaren Sinanci wajen gayyatar Sinawa zuwa kasarsa. Ya ce,"Sinawa na darajanta muhalli, sa'an nan a kasarmu Rwanda muna da muhalli mai kyau. Muna da naman daji, wadanda babu irinsu a sauran kasashe. Zuwa yawon shakatawa a Rwanda na da tsaro sosai, ko yanzu ma za a iya zuwa. " (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China