2020-09-09 15:50:51 cri |
Malam Dong Paoyue ke nan, dan kabilar Jingpo wanda yake kiwon tsutsotsi masu samar da siliki. Malamin yana rayuwa a wani kauye na 'yan kabilar Jingpo da ke gundumar Longchuan ta lardin Yunnan na kasar Sin. A baya ya dade yana noman rake da shinkafa, kafin daga bisani ya fara kiwon tsutsotsi masu samar da siliki, aikin da ya ninka kudin shigarsa, har ma ya gina sabon gida tare da sayen mota. (Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China