Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kama hanyar zama babbar kasuwar sayar da EVS a duniya
2020-09-09 17:19:26        cri

A yayin da wasu kasashen yamma ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, ita kuma kasar Sin ta riga ta yi adabo da wannan annoba, har ma a kwanakin baya ta shirya wani kasaitaccen bikin karrama 'yan kasar da suka ba da gagarumar gudummawa a yakin da baki dayan al'ummar Sinawa suka yi da wannan annoba, da yanzu haka ta yiwa bangarorin rayuwa na duniya daurin kazar kuku.

Yanzu haka dai harkokin masana'antu sun damo kamar yadda suke a baya a kusan daukacin sassan kasar Sin. Wani albishiri ma shi ne, cibiyar nan dake bincike kan harkokin da suka shafi motoci ta kasar Jamus (CAR) ta fitar da wani sabon rahoto dake nuna cewa, ya zuwa karshen wannan shekara, kasar Sin za ta kama hanyar sake zama babbar kasuwar sayar da motoci masu aiki da wutar lantarki (EVs) a duniya. Wai idan ba ka yi, ba ni wuri.

Hasashen cibiyar na nuna cewa, kasuwar irin wadannan motoci a yankin Turai a watanni shida na farkon bana, ta dan tashi, amma rawar da Elon Musk wani kwararre a fannin fasahar kere-keren zamani ya taka, za ta taimaka wajen bunkasa kasuwar kasar Sin, wadda ake ganin za ta ci gaba da jan ragamar kasuwar sayar da motoci masu aiki da wutar lantarki na wasu shekaru 50 masu zuwa.

A watanni shida na farkon bana, bayanai sun nuna cewa, an sayar da motoci masu aiki da wutar lantarki da baturan da ake caji kimanin 400,000 a Turai.

Duk mai bibiyar harkokin da suka shafi kerawa da sayar da motoci na zamani, yana jin labarin kamfanin Tesla, kamfanin da ya taka muhimmiyar rawa wajen fito da sunan kasar Sin a harkar motoci masu aiki da wutar lantarki. Alkaluma na nuna cewa, a watanni shida na farkon bana, kamfanin Tesla Shanghai giga, ya sayar da irin wadannan motoci kusan 50,000 a cikin kasar. Mai abu da abinsa, wai kura da kallabin kitso.

Masana na cewa, idan har wannan batu ya tabbata, hakika kasar Sin za ta cika alkawarin da ta yi, na rage wani kaso mai tarin yawa na hayaki masu gurbata muhalli da motoci ke fitarwa. Motoci masu aiki da wutar lantarki na ci gaba da samun karbuwa a duniya, matakin da masana ke ganin zai rage dogaro kan man fetur, baya ga rage gurbatar muhalli dake ciwa duniya tuwo a kwarya. Wanda ya riga ka barci, dole ya riga ka tashi. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China