Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an tsaron Australia sun yiwa wasu 'yan jarida Sinawa dirar mikiya
2020-09-09 21:53:08        cri
Wasu rahotanni na cewa cikin watan Yunin wannan shekarar da muke ciki, jami'an tsaron farin kaya na kasar Australia, sun yiwa wasu 'yan jaridar kasar Sin su hudu dirar mikiya, inda suka kwacewa 'yan jaridar na'urorin su na kwamfuta, da wayoyin salula da sauran kayan aiki.

Don gane da hakan, mai magana da yawun ma'aikatar wajen Sin Zhao Lijian, ya bayyana a taron manema labarai na rana-rana da aka saba gudanarwa na Larabar nan cewa, Sin na fatan jami'an tsaron Australia za su kauracewa aikata irin wannan matakai maras kyau a nan gaba, su kuma dakatar da cin zarafi ko musgunawa ma'aikata Sinawa bisa kowace irin manufa. Kaza lika Sin na kira gare su, da su tabbatar da kare lafiya da hakkoki na halas da Sinawa ke da su, kana su kaucewa shiga duk wasu al'amura masu nasaba da musaya tsakanin al'ummun Sin da na Australia, da ma harkokin hadin gwiwar kasashen biyu.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, dukkanin 'yan jarida Sinawa dake aiki a Australia, na kiyaye ka'idoji da dokokin kasar yadda ya kamata, suna kuma aiki bisa tsari ba tare da nuna wani bambanci ba, a yayin da suke zantawa da mutane ko shirya rahotanni. Ya ce abun da gwamnatin Australia ta yi, ya gurgunta tsarin aikin ba da rahotanni na kafofin Sin dake Australia, ya kuma yi matukar keta hakkoki da moriyar 'yan jarida Sinawa dake aiki a kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China