Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta inganta tsarin sanya ido kan cututtuka masu yaduwa
2020-09-10 10:52:02        cri

Kasar Sin ta bayyana kudiri na kara inganta tsarin sanya ido, kan cututtuka masu yaduwa da kiwon lafiyar gaggauwa na jama'a, a yayin da take hade bayanai da suka shafi kiwon klafiyar jama'a waje guda.

Jami'in a hukumar lafiyar ta kasar Sin Mao Qun'an, shi ne ya bayyana haka. Yana mai cewa, duk da cewa an cimma wasu nasarori ta hanyar amfani da tsarin kiwon lafiya na zamani, a hannu guda kuma,annobar COVID-19 ta bankado rauni da wasu kananan matsaloli a wannna fanni.

Ya kara da cewa, akwai matsaloli masu tarin yawa a tsarin gudanarwa, da ababan more rayuwa, da musayar bayanai, wadanda a cewarsa, akwai bukatar a nazarce su da nufin magance su.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China