Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malamai sun cancanci yabo da martabawa bisa gudummawar da suke baiwa ci gaban bil Adama
2020-09-10 19:47:05        cri

Yau Alhamis 10 ga watan nan na Satumba, rana ce ta malamai ta kasar Sin, wadda aka fara gudanar da bikin ta tun daga shekarar 1985. A wannan rana, shugabannin kasar Sin, da dalibai, da ma sauran al'ummar Sin, dukkansu na jinjinawa gudummawar malamai a dukkanin matakai na ba da ilimi.


Da yake yanzu kasar Sin na kara bude kofarta ga kasashen ketare, malamai daga sassan duniya na kara shigowa kasar ta Sin, domin ba da gudummawar su a fannonin samar da ci gaba daban daban, ciki hadda wannan muhimmiyar sana'a ta malanta.


Albarkacin wannan rana, dalibai kan gabatar da kyaututtuka ga malaman su, haka ma hukumomin makarantu, kwalejoji da jami'o'i, kan baiwa malamai kyaututtuka da sakwanni na taya murnar sake zagayowar wannan rana. A hannu guda kuma, a kan gudanar da makaloli, da taruka na karawa juna sani tsakanin malamai, da jami'ai, da dalibai dake wannan muhimmin sashi na koyo da koyarwa.


Hausawa kan ce "Ilimi shi ne gishirin zaman duniya", kuma sanin hakan ne ma ya sa tun fil azal, Sinawa ke martaba sana'ar malanta. A duk lokacin da ranar malamai ta kewayo a nan kasar Sin, shugabanni kan aike da sakon taya murna, da jinjinawa ga daukacin malaman kasar, bisa muhimmiyar gudummawar da suke bayarwa wajen raya ilimi. A bana ma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya malaman kasar Sin murnar wannan rana, yana mai waiwaye game da irin gudummawar da malaman sa suka ba shi, ta fannin horon zama managarcin mutum, wanda har kullum ke kimanta matsayin ilimi. Shugaban ya kuma ce, muddin ana son kaiwa ga cimma nasarar duk wani babban aiki bisa turba mai dorewa, to ya zama wajibi a dogara ga ilimi.

Ko shakka babu wannan batu haka yake, domin kuwa a tarihin duniya na da, da na yanzu, da ma hasashen inda duniya ta dosa, ba a taba yin wani lokaci da wata kasa, ko wata shiyyar duniya ta samu ci gaba ba tare da ilimi ba.


Ko da a wannan lokaci da duniya ke fuskantar kalubalen cutar numfashi ta COVID-19, malamai ba su yi kasa a gwiwa ba, inda a sassa da dama na duniya ciki hadda nan kasar Sin da kasashen Afirka, sun ci gaba da koyar da dalibai ta kafofin na'urori masu kwakwalwa, da sauran hanyoyi da aka kirkira masu dacewa da yanayin da aka shiga, na kandagarki da shawo kan annobar. Hakika malamai sun yi rawar gani a wannan lokaci mai tsanani, wanda ya kusan durkusar da dukkanin harkokin rayuwar al'ummun duniya baki daya.


Duniyar bil Adama ta samu sauye-sauye, da bunkasuwa a fannonin kiwon lafiya, da kimiyya da fasaha, da fasahohin sadarwa, da noma, da ci gaban masana'antu, da fannin binciken sararin samaniya, da tattalin arziki, da siyasa da dai sauransu, albarkacin gudummawar ilimi. Ashe ke nan fannin ilimi ya cancanci duk wata martabawa, da darajtawa da za a iya ba shi.

Kamar kuma yadda a nan kasar Sin wannan sana'a ta malanta ke samun yabo da martabawa, alal misali, shehun malami Zhong Nanshan, mai shekaru 84 da haihuwa, wanda ya samu "Lambar Yabo Ta Jamhuriyar Jama'ar Sin" a shekaranjiya 8 ga watan, shi ma wani tsohon malami ne da ya taba yin aiki a jami'ar koyon ilmin likitanci ta Guangzhou. Sannan madam Yu Yi, mai shekaru 91 da haihuwa, wata malama ce da ta yi aikin malanta a wata makarantar midil ta Shanghai kafin ya yi ritaya. A ran 17 ga watan Satumban shekarar 2019, shugaban kasar Sin ya sa hannu kan wani umarnin yaba mata "Malamar Jama'a". Ana fatan dukkanin sassan duniya ma za su kara rungumar malamai, da baiwa sana'ar malanta karin gudummawa, ta yadda sana'ar za ta ci gaba da share hanyar ci gaban bil Adama daga dukkanin fannoni. Har a kai ga ginin al'ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya, mai cike da zaman lafiya, walwala da jin dadin rayuwa ga kowa. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China