Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin cinikin hidima ya nuna Sin za ta ci gaba da bude kofa ga ketare
2020-09-10 20:05:30        cri

A jiya Laraba ne aka rufe bikin baje kolin hada hadar cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020 a nan birnin Beijing, bikin da ya kasance babban aikin tattalin arziki da ciniki na kasa da kasa, karo na farko da kasar Sin ta shirya, tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda aka fitar da manyan ayyuka 97, da dandalolin dake shafar kasa da kasa 19, da kuma sakamakon kirkire-kirkire 99 a cikin kwanaki shida da suka gabata.

Kana gaba daya, adadin yarjejeniyoyin da larduna, da jihohi, da birane, da manyan kamfanonin gwamnatin kasar, da kamfanonin hada-hadar kudi suka daddale ya kai 240. Ana iya cewa, an samu gagarumin sakamako yayin bikin, lamarin da shi ma ya nuna cewa, kasuwar kasar Sin tana da babban karfi a asirce, haka kuma tana jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa matuka.

Bisa matsayinta na kasa mafi girma ta biyu wajen shigo da cinikin hidima a duniya, har kullum kasar Sin tana ingiza ci gaban aikin ba da hidima a fadin duniya. Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, tun daga shekarar 2012, cinikin hidimar kasar Sin ya karu da kaso wajen 7.8 bisa dari a ko wace shekara, kuma saurin karuwarsa ya fi na matsakaicin saurin karuwar da ake da shi a sauran sassan duniya yawa.

A shekarar 2019, kwatankwacin adadin shige da fice na cinikin hidima na kasar Sin, ya kai sama da kudin Sin yuan biliyan 5400, wato aikin ba da hidima ya kai kaso 59.4 bisa dari, cikin daukacin karuwar tattalin arzikin kasar. Mataimakin darektan hukumar ciniki ta duniya Yi Xiaozhun, ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka babbar rawa a fannin ci gaban tattalin arzikin duniya. Kuma tana matukar taimakawa ci gaban cinikin hidimar duniya.

Abun da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne, yayin bikin baje kolin cinikin hidima, kasar Sin ta sanar da wasu muhimman matakai, da manufofi a jere, domin nuna goyon baya ga ci gaban cinikin hidima, da kuma kara bude kofa ga ketare, duk wadannan sun sake shaida yunkurin kasar Sin na kara bude kofa ga ketare, da ingiza cudanyar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, da kuma kara zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen duniya.

Jagoran kamfanin Deloitte mai kula da harkokin kamfanin dake yankin Asiya da tekun Pisifik, Mr. Thierry Delmarcelle ya furta cewa, kasar Sin ta yi nasarar kammala bikin baje kolin cinikin hidima, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da bude kasuwarta, kuma za ta ci gaba da kyautata muhallin kasuwancinta, haka kuma za ta ci gaba da bude kofa ga ketare a bangaren ba da hidima. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China