Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bincike: Shugabannin kamfanonin Afrika sun yi amanna cewa cinikayya a tsakanin nahiyar zai karu a watanni 12 masu zuwa
2020-09-11 14:49:18        cri

Sama da kashi 70 bisa 100 na manyan shugabannin kamfanoni a Afrika sun yi amanna cewa kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar zai bunkasa nan da watanni 12 masu zuwa, wani rahoton bincike da aka fitar ranar Alhamis ne ya bayyana hakan.

A cewar binciken cinikin Afrika na 2020, kasuwancin dake gudana tsakanin kasashen nahiyar bai wuce kaso 15 ba, kuma shi ne mafi karanci idan an kwatanta da na sauran shiyyoyin duniya, amma akwai damammaki na karin bunkasuwa.

Yarjejeniyar ciniki maras shinge ta nahiyar AfCFTA, ta kasance wata muhimmiyar hanyar bunkasa kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika, a cewar binciken, wanda kungiyar bunkasa kasuwanci da zuba jari mai zaman kanta ta Afrika PAFTRAC da bankin shigi da fici na Afreximbank suka gudanar.

Manyan shugabannin kamfanonin na Afrika sun nuna cewa, yarjejeniyar AfCFTA ta samar da wani yanayin ciniki domin inganta yin gogayya da samar da ingancin kayayyaki wanda zai yi matukar bunkasa cigaban tattalin arzikin Afrika wajen samun daukaka a tsarin tattalin arzikin duniya.

Rahoton binciken ya nuna cewa, bangarori masu zaman kansu a Afrika suna da matukar tasiri a harkokin cinikin kasa da kasa inda kashi 50 bisa 100 na shugabannin suka yi amanna cewa harkokin kasuwan duniya zai karu a cikin watanni 12 masu zuwa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China