Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin Amurka Na Korar Daliban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Tunanin McCarthy Ya Koma Amurka
2020-09-11 15:53:59        cri

 

Ran 9 ga watan nan, mai magana da yawun majalisar gudanarwa ta Amurka Morgan Ortagus ya nuna cewa, bisa kuduri mai lamba 10043 da shugaban kasar Donald Trump ya gabatar a ran 29 ga watan Mayu , har wa yau gwamnatin Amurka ta soke dubban takardun neman iznin shiga Amurka na dalibai da masu nazari na kasar Sin saboda a ganinta za su kawo barzana ga tsaron kasar. Amma a ran 27 ga watan Maris, a lokacin da shugabannin Sin da Amurka suka yi tattaunawa ta wayar tarho, bangaren Amurka ya ce, jama'ar Amurka na matukar mutunta da kuma son jama'ar kasar Sin, a don haka daliban kasar Sin na da muhimmanci sosai ga sha'anin ba da ilmi a kasar, kuma Amurka za ta kiyaye Sinawa da ma dalibanta dake kasar.

Ga abu ya faru a yanzu, Amurka ta yi amai ta lashe kan wannan batu.

 

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, jerin matakai marasa kyau da Amurka ta dauka a fannin musanyar al'adu sun saba tunanin bude kofa da 'yancin na Amurka, kuma ya sabawa ra'ayin jama'a da ma kawo cikas ga musanyar kwararru tsakanin ksashen duniya. Haka kuma matakin zai illata mu'amalar al'adu da jama'a tsakanin kasashen biyu, da ma tushen dangantakar kasashen biyu.

 

Ko wannan shi ne tunanin McCarthy, wanda ya yi kaurin suna a tarihi?

 

Amurka dai ta kori wadannan dalibai ne wai, bisa zarginsu da laifin leken asiri, wadanda suke da alaka da sojojin kasar Sin. Amma ikirarin na Amurka gaskiya ne?

 

Mujallar "Nature" ta Birtaniya ta yi nazari cewa, Amurka za ta yi asara a fannin kirkire-kirkire kan matakin da take dauka na korar dalibai da kuma Sinawa masu nazari, baya ga yadda Amurka ke bata sha'anin kimiyyarta. Steven Chu, tsohon ministan makamashi na Amurka, wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel a fannin ilmin kimiyyar kere-kere a shekarar 1997 ya ce, Amurka ba za ta zama kasa mafi girma a duniya a fannin kimiyya da fasaha da masana'antu da ma ilmin kimiyyar lissafi ba idan babu masu kimiyya da fasaha na ketare ko baki daga kasashen waje.

 

A hakika, dalibai Sinawa sun taka rawa wajen kara mu'ammala da fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen biyu tun kafuwar dangantakar diplomasiyyar kasashen biyu. Dalibai da kuma masu ilmi na kasar Sin sun ba da babbar gudummawa ga aikin kirkire-kirkire da ma bunkasuwar tattalin arzikin Amurka, yawan daliban Sin dake karatu a Amurka ya kai kashi 1 cikin 3 na dukkanin daliban ketare, yawan kudin da suke kashewa a kowace shekara ya kai dala biliyan 1.5.

To, don me Amurka ta yi watsi da daliban kasar Sin wadanda suke ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar Amurka? Watakila 'yan siyasar Amurka masu kan gado ne kawai suka san ainihin dalili. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China