Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tushen daidaita rikicin kan iyakar Sin da Indiya shi ne nacewa matsaya daya da suka cimma
2020-09-11 20:59:24        cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Indiya Subrahmanyam Jaishankar a jiya Alhamis, inda bangarorin biyu suka tattauna halin da kasashen su ke ciki game da batun kan iyakarsu, da ma dangantakarsu, inda suka kai ga cimma matsaya daya kan abubuwa biyar.

Bangarorin biyu sun cimma matsaya daya, a daidai wannan lokaci da dangantakarsu ta yi tsami, matakin da ya samar da dama mai kyau ta kyautata halin da ake ciki, da ma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar su.

A bana ne ake cika shekaru 70 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. A matsayinsu na kasashen da suka fi yawan mutane a duniya, kuma kasashe mafiya girma tsakanin kasashe masu tasowa, Sin da Indiya, na da nauyi iri daya a bisa wuyansu, wato tinkarar cutar COVID-19, da bunkasa tattalin arziki, da ma kyautata zaman rayuwar jama'a.

Ban da wannan kuma, suna da muradun bai daya, na kiyaye tsari da oda a duniya bisa tushen dokokin kasa da kasa, don haka, kamata ya yi bangarorin biyu su kara zurfafa hadin kansu, a maimakon yin fito-na-fito a tsakaninsu.

"Hadin kan kasashen biyu, ita ce hanya daya tilo da bangarorin biyu za su bi, don biyan muradun jama'ar su tun daga tushe." Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi, a watan Oktomba na shekarar 2019. A hakika dai, Sin da Indiya makwabciyar juna ce har abada, don hakan, ya kamata kasashen biyu su taimakawa juna.

Game da dangantakar kasashen biyu da ta yi tsami a yanzu kuwa, ya kamata Indiya ta yi hadin kai da kasar Sin, don cika alkawarin da ta yi, da kuma daukar matakan da suka dace, don kwantar da hankali a kan iyakarsu, bisa matsaya daya a fannoni biyar da suka cimma a wannan karo, ta yadda za a maido da kyakkyawar dangantakar kasashen biyu cikin sauri, da kiyaye zaman lafiya mai dorewa, da ma bunkasuwar shiyyar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China