Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zaman rayuwar manoma da makiyaya mai dadi a yankin Tibet
2020-09-12 20:19:43        cri
A shekarar 2016, Dekyi Wangmo ta koma garinta dake kauyen Tunbai na gundumar Milin na jihar Xizang mai cin gashin kanta da ke yammacin kasar Sin. Inda take ganin cewa, kasancewar garinsu a dab da kogin Brahmaputrada da kuma tudun Namcha Barwa, ya dace su yi amfani da albarkatun da suke da su don bunkasa harkokin yawon shakatawa.

Dekyi Wangmo ta ba da shawarar ga mazauna kauyen, wadanda suka nuna goyon bayansu sosai. Harkokin yawon shakatawa ya samu bunkasuwa sosai, har ma ya samar da karin guraben aikin yi ga mazauna kauyen.

Sai kuma a kauyen Jiuba, a baya, mazauna kauyen suna samun kudin shiga ne ta hanyar sare itatuwa da dibar laimar kwado da dai sauransu, amma yanzu an fara nazarin sha'anin shuke-shuke bayan an kyautata manufofi masu nasaba.

A shekarar 2009, an kafa kungiyar hadin kan manoma da makiyaya ta fuskar shuka strawberry, wadda ta shigo da mutane 60 da suke fama da talauci a ciki. Ta hanyar dogaro da wannan sha'anin, ba da dadewa ba dukannin mazauna kauyen sun fita daga kangin talauci.

Ganin yadda strawberry a kauyen ke jawo baki masu yawon bude ido, kauyen ya kuma fara bunkasa harkokin yawon shakatawa.

Kauyen Tunbai da ma Jiuba sun tattalin arzikinsu bisa muhalli da yanayin da suke ciki, matakin da ya fidda boyayyen karfin wurin wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, ta wannan hanya manoma da makiyaya sun fita daga kangin talauci har ma suna samun wadata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China