Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar tsaron Sin ya yi tsokaci kan rahoton aikin soja da tsaron kasar Sin da Amurka ta fitar
2020-09-13 16:12:22        cri

Yau kakakin watsa labarai na ma'aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian ya yi tsokaci kan "Rahoton ci gaban aikin soja da tsaro na kasar Sin na shekarar 2020" wanda Amurka ta fitar, inda ya bayyana cewa, rahoton wata shaida ce ta daban da Amurka ta shafawa kasar Sin da rundunar sojojin kasar bakin fenti, kuma matakin da Amurka ta dauka wato ta fitar da irin wannan rahoto a cikin shekaru 20 da suka gabata, nuna fin karfi da kawo barazana ne da take yiwa kasar Sin, ko shakka babu, zai lalata huldar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Amurka, don haka kasar Sin ta nuna rashin jin dadi da adawa ga matakin, haka kuma ta riga ta sanar da Amurka ra'ayin da ta dauka kan lamarin.

Wu Qian ya jaddada cewa, kasar Sin tana nacewa kan manufar samun ci gaba cikin lumana, kuma tana nacewa kan manufar tsaron kasa ta hanyar tabbatar da tsaronta, makasudin kara karfafa karfin aikin sojar kasar Sin shi ne domin kiyaye ikon mulkin kasa da tsaron kasa da bukatun samun ci gaba, ba zai yiwu ba ta kawo barazana ga sauran kasashen duniya.

Jami'in ya kara da cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, Amurka ta taba daukar matakan aikin soja kan kasashen Iraki da Syria da Libya da kuma sauran kasashen duniya, a sanadiyyar haka, adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai sama da dubu 800, kana mutane sama da miliyan goma sun rasa muhallansu. Hakikanin abubuwan da suka faru a cikin 'yan shekarun da suka gabata sun shaida cewa, Amurka ita ce kasa dake tayar da tarzoma a shiyyoyin duniya, kuma ita kasa ce dake lalata tsarin kasa da kasa da zaman lafiyar duniya.

Wu Qian, ya sake jaddada cewa, rundunar sojojin kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da muradun gina kyakkyawar makomar bil Adam, kuma za ta ci gaba da taka rawa a bangarorin shimfida zaman lafiya a fadin duniya da tabbatar da ci gaba a fadin duniya da kuma kiyaye tsarin kasa da kasa mai adalci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China