Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi a zurfafa yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha wajen biyan bukatun kasa
2020-09-13 20:21:41        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin ci gaba da bunkasa fannonin kimiyya da fasaha, don zurfafa biyan muhimman bukatun kasa.

Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne a birnin Beijing a kwanan nan, yayin wani taron karawa juna sani, wanda masana a fannin kimiyya da dama suka halarta.

Ya ce, ya dace fannonin kimiyya da fasaha na Sin, su shiga matakan kasa da kasa, don fafatawa a gwagwarmayar tattalin arziki, su kuma kara haifar da kyakkyawan sakamako ga bukatun kasa, da rayuwar al'ummunta, da fannin kiwon lafiyarsu. Shugaba Xi ya kuma sake nanata ma'anar gaggauta yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha, tare da bayyana fatansa ga masana kimiyya da fasahar kasar.

A 'yan shekarun nan, fannonin kimiyya da fasaha na kasar Sin suna samun dimbin nasarori da fuskantar wasu manyan sauye-sauye, abun da ya sa kasar ta kasance kan gaba a wasu fannonin kimiyya da fasaha a duk fadin duniya, ciki har da fasahar noma, da fasahar gina gadoji, da fasahar sadarwar 5G, da fasahar shimfida layin dogo mai saurin gaske, da fasahar nazarin sararin samaniya da sauransu. Amma kamata ya yi a ci gaba da inganta karfin kasar na yin kirkire-kirkire, duba da halin sarkakkiya da ake ciki a gida da waje wajen samun bunkasuwa.

A yayin da ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci ke ci gaba da yaduwa a duk duniya, ya zama dole kasar Sin ta lalibo wata sabuwar hanyar da ta dace wajen yin kirkire-kirkire, domin kara samun fahimta a wadannan fannoni ya kamata a maida hankali wajen yin kirkire-kirkire, ta yadda kasar Sin za ta samu babbar nasara wajen nazarin wasu fannonin kimiyya da fasaha masu matukar muhimmanci a duniya.

Har wa yau, zurfafa yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha na bukatar kwazon aikin masana kimiyya da fasaha. Shugaba Xi ya bukaci masu kula da fannin kimiyya da fasaha su mayar da muradun kasa da moriyar jama'a a gaban kome, da ci gaba da yayata kyawawan dabi'un wasu tsoffin masana kimiyya da fasaha, wato kishin kasa da bautawa al'ummar kasar. Sa'annan ya kamata su nuna jarumta wajen lalibo sabbin hanyoyin nazarin kimiyya da fasaha, da nuna himma da kwazo wajen gudanar da aikinsu ba tare da kasala ba.

A halin yanzu, duniya na fuskantar manyan sauye-sauyen da ba'a taba ganin irinsu ba a tarihi, kuma yanayin da ake ciki a gida da waje yana canjawa a koda yaushe, al'ummar kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4 za su kama hanyar raya kasa mai tsarin gurguzu irin na zamani daga dukkan fannoni. Shi ya sa a daidai wannan muhimmin lokaci, akwai babban nauyi da kuma jan aiki a wuyan masana kimiyya da fasahar kasar. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China