Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka harbu da COVID-19 a fadin duniya a rana guda ya yi tashin gwauron zabi
2020-09-14 13:26:22        cri

Alkaluman kididdiga na hukumar lafiya ta duniya WHO, sun nuna matukar karuwar da aka samu, ta masu harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a kwana guda, inda alkaluman na jiya Lahadi suka nuna cewa, cikin sa'o'i 24, mutane 307,930 sun harbu, adadin da ya kasance mafi yawa a rana daya tun barkewar cutar.

Ya zuwa jiyan, jimillar wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum 28,637,952, kana adadin wadanda cutar ta hallaka ya karu da mutum 5,537, inda ya kai jimillar mutum 917,417, yayin da adadin masu harbuwa da cutar ke hauhawa, musamman a kasashen Amurka, da India, da Brazil da Rasha. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China