Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Amurka ta yi hannun riga da hadin gwiwar kasa da kasa kan COVID-19
2020-09-14 19:52:44        cri

Kasar Sin ta yi maraba da yadda kudurin MDD kan matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ya samu amincewa a babban zauren MDD. Tana mai cewa, hakan wata manuniya ce kan yadda kasashen duniya suka yi na'am da hadin gwiwar bangarori daban-daban da ma yin hadin gwiwa, a matsayin hanya daya tilo ta magance kalubalolin dake addabar duniya.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, shi ne ya bayyana haka, lokacin da yake karin haske kan kuri'ar goyon bayan da mambobin majalisar 169 cikin 193 suka kada, Jumma'ar da ta gabata, sabanin kasashen Amurka da Isra'ila da suka ki goyon bayan kudirin.

Kudirin dai ya bayyana cewa, annobar COVID-19 ta haifar wa duniya manyan kalubaloli da ba a taba gani ba a tarihin majalisar, a don haka, ta yi kira ga kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa da sadaukar da kai wajen ganin baya da ma jure tasirin annobar.

Wang ya yi nuni da cewa, wannan ya nuna yadda kasashe da suka san abin da ya dace suke kokarin ganin bayan matsalar da ta addabi kowa. Inda ya yi misali da yadda Amurka ta gaza dakatar da wannan kudiri. Yana mai cewa, janyewar Amurka daga kungiyoyin kasa da kasa, da yadda ta ke yiwa hadin gwiwar kasashen duniya kan yaki da COVID-19 zagon kasa, bai samu karbuwa ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China