Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin zirga zirga a cikin kasar Sin zai kai biliyan 3.4
2020-09-15 10:11:13        cri

Wani rahoton kididdiga da cibiyar lura da harkokin yawon shakatawa ta Sin ta fitar, ya nuna cewa, adadin zirga zirga da Sinawa za su yi a cikin kasar a bana zai kai biliyan 3.4, adadin da ya ragu da kaso 43 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara.

Rahoton wanda cibiyar ta fitar a ranar Litinin, ya ce Sin za ta samu kudaden shiga da yawan su ya kai yuan tiriliyan 2.76, kimanin dalar Amurka biliyan 400 ta harajin cikin gida a fannin yawon bude ido a shekarar ta 2020, adadin da ya yi kasa da na shekarar da ta gabaci hakan da kaso 52 bisa dari, sakamakon bullar cutar numfashi ta COVID-19.

Kaza lika rahoton ya ce, sashen yawon bude ido na kasar Sin na kara farfadowa cikin sauri, inda kaso 80 bisa dari na Sinawa ke bayyana aniyar su ta yin tafiye tafiye cikin watanni uku na rubu'i na uku, sabanin kaso 90 bisa dari da aka samu a makamancin lokaci na shekarar 2019. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China