Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar MDD: Tilas ne a magance matsalolin rashin daidaito a lokacin yaduwar cutar COVID-19 da ma bayan cutar
2020-09-15 10:49:43        cri
Jami'ar majalisar kare hakkin bil adama ta MDD ta ce, yaduwar annobar COVID-19 da dunbun kalubalolin da annobar ta haifar yana da alaka mai karfi da batun banbancin jinsi, da kabilanci, da matsayin tattalin arziki, gami da samun kyakkyawan sakamako a fannin kiwon lafiya, tilas ne a yi kokarin kawar da kalubalolin domin gina ingantaccen muhallin rayuwar bil adama a duniya.

Da take jawabi a rana ta farko a taron majalisar kare hakkin bil adama ta MDD karo na 45, kwamishiniyar kare hakkin dan adam ta MDDr, Michelle Bachelet, ta ce, majalisar za ta tattauna game da yadda manufofin kare hakkin dan adam din za su taimaka wajen daidaita tasirin wannan annoba.

Jami'ar ta ce, kasashen duniya da dama sun yi nasarar aiwatar da wasu tsare tsare dake shafar muhimman bangarorin kare hakkin dan adam, kamar fannin kiwon lafiya, da baiwa al'umma kariya. Muhimmancin gabatar da wannan tsarin kare hakkin dan adam ba zai taba misaltuwa ba.

Shugabar hukumar kare hakkin ta MDD ta kara da cewa, a halin da ake ciki a yanzu, kula da lafiyar al'umma muhimmiyar hanya ce ta baiwa al'umma kariya, kare mutane daga bala'in talauci, da samar musu muhimman kayayyakin more rayuwa da tabbatar da hakkin bil adma a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China