Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karya fure take, bata 'ya'ya
2020-09-15 20:31:26        cri

Wani masani dake aiki a jami'ar Xinjiang farfesa Lin Fangfei, ya fitar da sakamakon bincike da ya gudanar, game da yawan al'ummar jihar Xinjiang.

Rahoton mai taken "Martani ga karairayin Adrian Zenz game da kayyade iyali a Xinjiang: bincike game da damar haihuwa ga matan kananan kabilu na jihar Xinjiang," ya soki karairayi, da jita-jita da ake yadawa game da yawan al'ummar dake zaune a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta.

Wannan bincike ya zo a kan gaba duba da yadda kafafen watsa labarai na kasashen yamma ke ci gaba da yada jita-jita kan yadda kasar Sin ke tafiyar da al'ummar jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin.

Gwamnatin kasar Sin gwamnati ce da ta yi fice wajen aiwatar da kyawawan manufofi da matakan inganta rayuwar al'ummarta. Duk yadda mutum ya kai ga kin jinin kasar Sin, ba zai taba cewa ba ta kula da al'ummarta ba. A hakika ma dai, duk wani abu da kasar Sin za ta yi, ta kan duba yadda zai amfani al'ummarta ne, kuma a duk abun da za ta yi, ta kan ba su fifiko sama da komai, kana ba ta banbanta su.

Sanin kowa ne cewa kasar Sin ta fi kowacce kasa yawan al'umma a duniya. Kuma tsarin kayyade iyali, batu ne da aka kirkiro shi gomman shekaru da suka gabata, ba wai a yau ba. Kana ba batu ne da ya mayar da hankali musammam kan wata kabila ba.

Kasar Sin ta kaddamar da tsarin haihuwar da daya ne ga kowanne iyali tun cikin shekarar 1979, kuma ta gyara shi a shekarun 1980, domin ba mazauna yankunan karkara haihuwar 'ya'ya 2 idan an haifi 'ya mace da farko. sannnan kuma a shekarar 2015, ta sake dawo da tsarin haihuwar 'ya'ya biyu ga kowanne iyali dake muradi, sannan ta kara gyara wasu manufofi a hukumomi da kamfanoni, domin ba mata ma'aikata kwarin gwiwar kara haihuwar.

Abun mamaki shi ne, yawancin iyalai ma ba sa son kara haihuwar 'ya'yan, sun fi son haihuwar da daya ko ma rashinsa baki daya. Sai dai a baya bayan nan, kafafen watsa labarai na yammacin duniya, na yayata manufofin kasashensu na son bata sunan gwamnatin kasar Sin a idon duniya, inda suke sukarta da cewa wai tana tilastawa matan kabilar Xinjiang kayyade iyali.

Abun takaici shi ne, yadda wadancan kasashe ko jami'ansu ko kafafen watsa labaransu ke yada jita-jita ba tare da bin diddigi ko gudanar da binciken kwakwaf ba. Ya kamata a duk lokacin da wani zai yi suka ko nuna yatsa ga wani, ya tabbatar yana da shaidu masu kwari da za su goyi bayan ikirarin da ya yi. Shin 'yan kabilar Uygur ne kadai al'ummar kasar Sin? Me ya sa ba a tada jijiyoyin wuya kan sauran kabilun kasar da dukkansu ka'idar kayyade haihuwar ta shafa? Cikin kabilu 56 dake akwai a kasar Sin, kimanin goma mabiya addinin Musulunci ne, idan saboda addini kasar ta fitar da waccan manufa, me ya sa ba ta shafi sauran kabilun ba sai ta Uygur?

Duk mai hankali ya san cewa, kasar Sin kasa ce dake da zaman lafiya da karancin laifuffuka idan aka kwatanta da sauran kasashen da suka ci gaba irinta. Kuma wannan ba ya rasa nasaba da kyawawan manufofinta kan al'ummarta, ciki har da kokarin rage yadda ake samun karuwar al'ummma. Bahaushe ma ya ce idan dambu ya yi, baya jin mai. A ganina, matakin nata na bisa turba, domin dukkan al'ummarta na cin gajiyar duk wani abu da ta yi dominsu, koma tana iya bakin kokarin ganin ta fitar da su daga kangin talauci domin su rayu cikin wadata, kuma ko kadan, ba ta ware wani rukuni ko kabila ko mabiya addini ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China