Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: Tattalin arzikin Sin na kan hanyar samun tagomashi a bana
2020-09-16 10:41:37        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce ga dukkanin alamu, kasar sa za ta cimma nasarorin tattalin arziki da ta tsara a bana, tare da samun karuwar GDP. Li ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa na musamman da manyan 'yan kasuwa na duniya, wanda ya gudana jiya Talata ta kafar bidiyo.

Firaministan na Sin ya kara da cewa, Sin ta cimma nasarar hanzarta dakile cutar COVID-19, tare da tabbatar da samuwar muhimman ababen more rayuwar jama'ar ta, ko da yake wannan aiki a cewar sa, ba abu ne mai sauki ba, ga kasa mai tasowa dake da yawan al'umma da ya kai mutum biliyan 1.4.

Ya ce a halin da ake ciki, tattalin arzikin Sin na bunkasa, har ma an kai ga cimma nasarar samar da sabbin guraben ayyukan yi sama da miliyan bakwai, a yankunan birane da karkara daga farkon shekara zuwa yanzu.

Firaministan na Sin ya kuma yi kira ga sassan duniya da su kara azama, wajen shawo kan hadurra da kuma kalubaloli. Ya ce babban kalubalen dake gaban duniya a halin yanzu, shi ne tabbatar da shawo kan yaduwar wannan cuta, da farfado da tattalin arziki.

Daga nan sai ya jaddada cewa, sakamakon tarin rashin tabbas da ake fuskanta, za a shafe tsawon lokaci kafin tattalin arzikin duniya ya farfado daga komadar da ya shiga.

Taron wanda dandalin tattalin arziki na duniya ko WEF ya shirya, ya samu halartar sama da manyan 'yan kasuwa 500. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China