Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta musanta shirin kashe jakadan Amurka dake Afrika ta Kudu
2020-09-16 10:44:31        cri
Kwanan baya, wasu kafofin yada labarai na kasar Amurka sun ruwaito maganar majiyoyin da ke da masaniya na cewa, gwamnatin Iran tana tunanin hallaka jakadan Amurka dake Afrika ta Kudu.

Kuma game da hakan, shugaban Amurka Donald Trump, ya wallafa a shafin sa na yanar gizo cewa, mai yiwuwa Iran din na shirin kashe Amurkawa, ko kaddamar da hari, a matsayin mayar da martani ga kisan janar din sojan ta Qasem Soleimani. Don haka ya yi barzanar cewa, idan har Iran ta dauki irin wannan mataki, to Amurka za ta mayar da martani mai tsanani.

To sai dai kuma a daya bangaren, a jiya Talata 15 ga watan nan, mai magana da yawun gwamnatin Iran Ali Rabiei, ya musanta wannan labari, yana mai cewa, gwamnatin Amurka ta saurara, da kuma amincewa da wannan jita-jita ne kila duk domin cimma bukatunta na babban zabe.

Ya ce, idan an waiwayi tarihin yankin gabas ta tsakiya, ana iya ganin cewa, gwamnatin Amurka ce ta fara yakin Afghanistan, da Iraqi, duk bisa labarai na karya. Don haka ba za a yarda da mataki mai cike da hadari da gwamnatin Amurka ke shirin dauka ba, matakin ne na tada hankalin shiyyar don neman samun nasara a babban zabe.

Jami'in ya kara da cewa, yana fatan gwamnatin Amurka ba za ta yi sabon kuskure game da matakan da za ta dauka kan Iran ba, inda kuwa ta aikata hakan, Iran za ta mayar da martani. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China