Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Xining na lardin Qinghai ya ba da tabbaci ga iyalai masu fama da talauci
2020-09-16 14:21:31        cri

Birnin Xining, hedkwatar lardin Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin, yana bin manufar ba da taimako bisa karfin al'umma, da ba da ceto ga wadanda ke fuskantar matsalolin gaggawa, da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a, da kuma inganta zaman adalci, inda ya shigar da wadanda suka nakasa mai tsanani, da wadanda suka kamu da cututtuka masu tsanani na iyalai masu fama da talauci a cikin tsarin ba da tabbaci, yana ta kuma yin namijin kokari don taimakawa rukunin musamman na fuskantar wahalhalu dake birnin wajen warware matsalolin da suke fuskanta.

Ma Jinxiao, 'dan shekaru 53 a duniya, wanda ya gamu da wahalhalu masu yawa a zaman rayuwarsa. A yayin da yake da shekaru 17 a haihuwa, kwakwalwarsa ta ji rauni mai tsanani sakamakon wani hadarin da aka samu ba zato ba tsamani, hakan ya sa ya samu shanyewar rabin jiki, gabar hannunsa ma ta nakasa sosai. Amma, duk da haka yana cike da iamani kan zaman rayuwarsa.

"A lokacin, na yi ta kokarin neman ci gaba, da hannu guda daya kawai na koyi hawan keke, daga baya kuma, na koyi yadda ake sayar da kayan lambu, na kan hau keke tare da daukar kayan lambu masu nauyin kilo 10 zuwa 25, a wasu lokuta ma har nauyin su kan kai kimanin kilo 130."

Dogara ga kokarin da ya yi da kyakkyawan fata da ya nuna, Ma Jinxiao ya yi aure, har sun haifi yara biyu, kuma suna zaune tare da mahaifiyarsa. Wane ne zai yi tunanin cewa, masifa za ta sake fado masa. A shekarar 2016, 'yarsa ta kamu da ciwo mai tsanani, Ma Jinxiao ya nemi shawarar likita kuma ya kashe duk kuɗin da suka tattara.

"A shekarar 2016, a karo na farko, 'ya ta ta yi ciwon zubar jini sakamakon raguwar irin abubuwan dake cikin jini, wadanda ke sa jini ya bushe in an samu rauni wato thrombocytopenic da Turanci. Mun rika kashe yuan 200 domin sayen magani a ko wane kwana biyu. Baya ga haka, ni da mata ta mun kamu da ciwon hawan jini, ni kuma na gamu da karancin isasshen jini a kwakwalwa, mata ta tana fama da ciwon zuciya, da na kashin baya mai matse jijiyoyi. Gaskiya, mun fuskanci babban nauyi a fannin tattalin arziki."

Dukkan kudin da iyalin Ma Jinxiao ke bukata a fannonin ganin likita, sayen magani, da kuma zaman rayuwa, suna dogaro da 'dansu dake aikin wucin gadi a waje. Kudin samun jinya masu yawa ya kara tsananta halin da wannan iyali marasa arziki ke ciki. A daidai wannan lokaci, gwamnatin wurin ta ba su taimako.

"A shekarar 2016, mun gabatar da rokon neman tabbaci bisa matsayin zaman rayuwa mafi kankanta, kuma mun rika samun tallafin kudi sama da yuan 2000. Baya ga haka, mun samu tallafin kudi a fannin aikin jinya yuan dubu 10. Ban da wannan kuma, gwamnatinmu ta ba mu wasu tikitin sayen kayayyaki da dai sauransu."

A kan wani gidan ajiye tufafi dake da aljihu biyar dake dakin falo na gidan Ma Jinxiao, an ajiye wani littafin taimako na nuna kauna, inda aka rubuta manufofin ba da tabbaci a fannoni daban daban, ciki har da samar da kudin tallafi yuan 2,000 domin bikin bazara, da kuma taimako na dan lokaci na yuan 17,396.48 don yanayin sanyi na bana da yanayin bazara na shekara mai zuwa, da tallafin kudi domin farashin kaya yuan 3,000 a tsakanin watan Janairu zuwa na Yuli, da dai sauransu, saboda daidai wadannan matakan ba da taimako ne, aka sanya iyalin Ma Jinxiao ya sake komowa hanyar zaman rayuwarsu yadda ya kamata.

A farkon shekarar 2018, Ma Jinxiao ya samu gidan haya na jama'a ta hanyar ba da roko, bisa manufar da aka tsara a fannin, wato gidaje bisa matsayin zaman rayuwa mafi kankanta sun iya rage kudin haya da kashi 90 cikin 100, haka Ma Jinxiao na bukatar biyan kudin haya yuan kimanin 70 kawai a ko wane wata. Ma Jinxiao, wanda ke sa rai ga rayuwa, shi ma yana da sabbin tsare-tsare. Yanzu dai yana shirin fara kasuwanci da matarsa.

"Ni da mata ta muna shirin bude wani karamin dakin cin abinci, ko kuma karamin shago, yanzu muna neman dakin da ya dace. A ko da yaushe ina cike da imanin cewa, babu wata matsala da ba za a iya wuce ta ba, lokacin da abubuwa suka bayyana, rana za ta haska rayuwa." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China