Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da Rasha za su nace wa bunkasa dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata
2020-09-17 14:15:23        cri

Jiya Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da manema labarai, lokacin da ya kammala aikinsa na taron majalisar ministocin kasashen waje, na kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai wato SCO, da kuma kawo karshen ziyarar kasashen Rasha, da Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da kuma Mongolia.

Yayin da ya tabo maganar dangantakar Sin da Rasha, Wang ya nanata cewa, dangantakar kut da kut ta Sin da Rasha, na da ma'ana matuka wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyya-shiyya, da ma kasa da kasa, a daidai wannan lokacin da duniya ke samun sauye sauye da kwaskwarima.

Wang ya ce, a karon farko, shugabannin kasashen Sin da Rasha sun gana da juna bayan bullowar cutar COVID-19. Kuma hadaddiyar sanarwar da minitocin wajen kasashen biyu suka gabatar, ta bayyana matsaya daya da bangarorin biyu, da ma duk fadin duniya ke dauka game da harkokin kasa da kasa.

Jami'in ya kuma yi nuni da cewa, yanzu haka kasashen duniya na fuskatar jarrabawa da tarihi ke nunawa. Wasu kasashe suna daukar matakin babakare da manufar kare kai, tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, da kuma matsawa Sin da Rasha lamba, da illata halin tsaro dake kewayen kasashen biyu.

Ya ce, hadin kan kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, ba zai canja ba ko kadan, ko da kuwa za a fuskanci duk wasu sauye-sauye. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China