Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron tattaunawa game da wanzar da kudurorin ci gaba na MDD da kwarewar Sin game da yaki da fatara
2020-09-17 17:12:41        cri

A gabar da ake cika shekaru 75 da kafuwar MDD, majalissar ta gudanar da wani taro ta kafar bidiyo, game da matakan wanzar da ci gaba mai dorewa, da kuma kwarewar da Sin ta samu a fannin yaki da talauci nan zuwa shekarar 2030.

Cikin mahalarta taron, akwai wakilai daga kasashe da yankuna 39, da kuma tsaffin 'yan siyasa 140, da wakilai na hukumomin kasa da kasa da masana, wadanda suka yi musayar yawu game da kwarewar da Sin ta nuna a fannin yaki da fatara, da matasayin da duniya ke ciki game da hakan, matakin da ake fatan zai ingiza tattaunawa game da dabarun cimma nasarar kudurorin ci gaba mai dorewa na MDD.

Tsohon babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya jaddada tasirin ci gaban kasar Sin mai matukar ban mamaki, wanda ya taka rawa wajen ingiza nasarar kudurorin ci gaban karni na MDD a matakin kasa da kasa.

A nasa bangaren, shugaban CMC Shen Haixiong, ya jaddada muhimmancin ci gaban harkar watsa labarai cikin lumana, musamman a fannin yaki da fatara, da bukatar yin hadin gwiwa da kafafen watsa labarai bisa tsari, wanda hakan ya yi babban tasiri ga aikin tsame miliyoyin Sinawa daga kangin talauci.

Shen Haixiong, ya kara da cewa, kirkire-kirkire a fannin watsa labarai, sun taimakawa aikin samar da managartan bayanai na yaki da fatara, kuma kwarewar Sin a fannin ta samar da dama ga dukkanin sassa, na shiga a dama da su wajen cin gajiyar wannan fa'ida.

A nasa tsokaci kuwa, wakilin kasar Afirka ta kudu, kuma ministan hadin gwiwa da cudanyar kasar da sauran kasashe Mr. Grobler, cewa ya yi, Sin ta yi rawar gani wajen tallafawa ci gaban nahiyar Afirka, kuma nahiyar ta gamsu da salon ci gaban kasar Sin, ta kuma koyi wasu dabaru daga kasar ta Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China