Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka sun gaza cimma wata karya da suka kitsa
2020-09-17 21:29:51        cri

A yau Alhamis ne kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi ayyukan yi, da hakkokin 'yan kwadago a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, alkaluman da aka fitar a cikin takardar sun nuna cewa, gwamantin jihar tana martaba yunkurin aiki na 'yan kwadagon jihar, tana kuma tabbatar da hakkokinsu bisa doka. Ana iya cewa, 'yan siyasar kasar Amurka sun gaza cimma wata karyar da suka kitsa, wai ana tilastawa al'ummun jihar Xinjiang yin aikin dole.

Duk da cewa, tattalin arzikin jihar Xinjiang bai samu ci gaba cikin sauri ba, haka kuma wasu yankunan dake kudancin jihar suna fama da kangin talauci, amma gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofi a jere domin tabbatar da samar da guraben aikin yi ga mazauna jihar, ta yadda za a kubutar da su daga talauci mai tsanani, alal misali, samar da guraben aikin yi kai tsaye, da kafa dandalin samar da bayanai, da samar da horo ga mazauna jihar domin su samu kwarewar aiki, da sauransu, kana gwamnatin jihar ta fitar da manufar yin kaura zuwa wani wuri na daban domin samun aikin yi a can, gaba daya adadin mutanen da suka samu aikin yi bisa wannan shirin, ya kai dubu 135 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019, lamarin da ya kara kudin shigarsu a bayyane.

Hakazalika ana tabbatar da kare hakkokin 'yan kwadagon jihar Xinjiang saboda su ma 'yan kwadago ne dake cikin daukacin 'yan kwadagon kasar Sin baki daya, musamman ma wajen 'yancin bin addini da yin amfani da yaren kabilunsu. Abun da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne, 'yan kwadagon jihar Xinjiang dake aiki a sauran sassan kasar ta Sin su ma suna jin dadin rayuwarsu, saboda a ko ina ana kare al'adunsu da 'yancinsu na bin addini da yin amfanin da yarensu, ta yaya za a baza jita-jita cewa, an tilasta musu domin su yi aiki?

Hakika babu ma'aunin da zai dace da yanayin daukacin kasashen duniya yayin da suke kokarin kiyaye hakkin bil Adam, bangaren kasar Sin ba ya bukatar a koya masa wani abu, haka kuma bai amince a yi amfani da ma'auni iri biyu ba, a don haka, kasar Sin tana fatan 'yan siyasar Amurka za su martaba hakikanan shaidu, haka kuma su daina siyasantar da duk wani lamari.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China