Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da kungiyoyin raya al'umma sun zanta game da dabarun yaki da talauci
2020-09-18 10:07:18        cri

Wakilan kungiyoyin raya al'umma 12 dake ayyukan su a kasashen Sin da Cambodia, da Mongolia, da Habasha, da ma wasu karin kungiyoyin kasa da kasa, sun zanta ta kafar bidiyo, game da kwarewar da Sin ta samu a fannin yaki da fatara.

Yayin taron na jiya Alhamis, wanda kungiyar CNIE mai rajin bunkasa musaya tsakanin sassan kasa da kasa ta Sin ta shirya, bangarorin sun karawa juna sani, game da tasirin kudurorin wanzar da ci gaba na MDD nan zuwa shekarar 2030, da kwarewar da aka samu game da yaki da fatara a mataki na kasa da kasa.

Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin babban sakataren CNIE Liu Lujun, ya ce ayyukan da Sin ta gudanar a fannin yaki da fatara, baya ga cika burikan Sinawa da suka yi, sun kuma ingiza ci gaban muradun samar da ci gaba mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030, da ma ci gaban jagoranci a fannin kare hakkin bil Adama.

Shi ma mataimakin shugaban cibiyar Sin ta yaki da fatara Tan Weiping, cewa ya yi Sin ta cimma manyan nasarori a fannin rage talauci, wanda hakan ke shaida karfin jagorancin JKS, da salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na Sin, tare da gabatarwa duniya dabarun yaki da talauci masu inganci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China