Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bincike: Amurkawa sun dena gaskata shugabanninsu da hukumomin yaki da COVID-19 na kasar
2020-09-18 10:37:56        cri

Wani bincike na baya bayan nan da aka gudanar kan wasu daidaikun mutane sama da 21,000 tsakanin 7 zuwa 26 ga watan Ogasta ya nuna cewa, jama'ar kasar Amurka sun yanke kauna da kuma kin yarda da gwamnatin kasar da hukumomi 15 dake tafiyar da ayyukan yaki da annobar COVID-19, an fara samun rashin yardar ne tun daga watan Afrilu har zuwa Ogasta, kamar yadda labaran da aka watsa a shafin intanet na jami'ar Northwestern University NU ya bayyana a ranar Laraba.

Yadda mutanen kasar suka dena yarda da yadda shugaban kasar Donald Trump ke tafiyar da ayyukan yaki da annobar COVID-19 ya ragu daga kashi 50% a karshen watan Afrilu zuwa kashi 43% a watan Ogasta, koda yake, adadin ya dan karu da maki biyu daga watan Yuli.

Rashin yardar ya faru ne game da cece-ku-cen da Amurkawa ke yi game da ko Amurkawan za su karbi rigakafin annobar COVID-19 idan an samar da shi. Mutane 6 cikin 10 ko kuma kashi 59 bisa na binciken da aka gudanar sun bayyana cewa, za su amshi rigakafin na COVID-19, an samu raguwar maki 7 daga kashi 66% a karshen watan Yuli.

Bambance-bambance game da wanda ya dace a yiwa rigakafin yana da alaka ta kut-da-kut da yadda mutane suka amince da shugabanni da kuma cibiyoyin yaki da annobar a kasar. Mutanen da suka ce sun aminta da shugaba Trump suna da niyya mafi karanci na karbar rigakafin annobar ta COVID-19.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China