2020-09-18 10:47:42 cri |
Jami'in ya yi kiran ne yayin taro na 10, na manyan wakilan kasashen BRICS, game da batun tsaro wanda ya gudana ta kafar bidiyo. Ya ce yayin da ake tunkarar kalubalen cutar COVID-19, kasashen BRICS wato Brazil, da Rasha, da India, da Sin da Afrika ta kudu, sun nuna matukar jajircewa wajen yin hadin kai tare, don shawo kan wahalhalu masu tsanani da ake fuskanta.
Yang ya ce daukar matakai na kashin kai, da kariyar cinikayya, da nuna fin karfi, suna lahanta alakar kasashe, da tsaro a matakin kasa da kasa. Don haka ya zama wajibi kasashen kungiyar BRICS, su yi amfani da wannan gaba da MDD ke cika shekaru 75 da kafuwa, a matsayin damar kara rungumar manufofin ba da kariya ga ka'idojin MDD, da aiki tare wajen yayata manufar BRICS, ta wanzar da cudanyar dukkanin sassa yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China