Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ya kamata Sin ta mallaki kimiya mai tushe
2020-09-18 14:04:36        cri

Jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da rangadin aiki a lardin Hunan. Yayin da ya ziyarci kamfanin samar da na'urori dake Changsha a wannan rana, ya bayyana cewa, kamata ya yi Sin ta mallaki kimiya daga tushe a hannunta, da ma sha'anin samar da kayayyaki.

Yayin da ya ziyarci kamfanin Sunward, wani kamfanin samar da na'urori, da aka kafa shekaru 21 da suka gabata, ya yi nazari tare da samar da na'urori fiye da 200 dake da 'yancin mallakar fasaha da karfin takara, ya kuma fitar da kayayyaki zuwa kasashe da yankuna fiye da 100, ya kuma shiga rukunin kamfanoni 50 da suka shahara wajen samar da kayayyaki a duniya, kana kamfanin dake cikin rukunin kamfanoni 20 a duniya dake kan gaba wajen samar da motar haka kasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China