Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Sin tana taka babbar rawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya
2020-09-18 20:46:33        cri

A yau Jumma'a a karo na farko gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayanai mai taken "yadda rundunar sojojin kasar Sin ta shiga aikin kiyaye zaman lafiyar MDD a cikin shekaru 30 da suka gabata", inda aka waiwayi ayyukan kiyaye zaman lafiyar da sojojin kasar Sin suka gudanar a cikin wadannan shekaru 30, kuma aka bayyana manufofin rundunar sojojin kasar na kiyaye zaman lafiya, da sakamakon da suka samu. Alkaluman da aka fitar a cikin takardar sun nuna cewa, rundunar sojojin kasar Sin tana taka babbar rawa kan aikin kiyaye zaman lafiyar MDD, takardar ta kuma mayar da martani ga jita-jitar da 'yan siyasar Amurka suka kitsa wai kasar Sin tana kawo wa kasashen duniya barazana a bangaren aikin soja.

Hakika kasar Sin tana kara taka rawa kan aikin kiyaye zaman lafya na MDD sakamakon sauye-sauyen da duniya ke fuskanta da bukatun aikin MDD, musamman ma tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawura guda shida na goyon bayan aikin MDD yayin taron kolin MDD a watan Satumban shekarar 2015, rundunar sojojin kasar Sin ta kara nuna himma da kwazo domin cimma muradun gina kyakkyawar makomar bil Adam.

Abun faranta rai shi ne, kokarin da rundunar sojojin kasar Sin ta yi ya samu amincewa daga MDD da zaman takewar al'ummun kasa da kasa, har mataimakin babban sakataren MDD Atul Khare ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana taka rawar gani wajen kiyaye zaman lafiya da tabbatar da manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban.

A halin yanzu, ya dace kasashen duniya su sauke nauyin dake bisa wuyansu domin kiyaye zaman lafiya a fadin duniya, amma wasu 'yan siyasar Amurka suna shafawa kasar Sin bakin fenti, har ma suna lalata tsarin kasa da kasa,

Bana shekaru 75 ke nan da kafa MDD, a don haka ya zama wajibi a kara darajanta zaman lafiya, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar samun ci gaba cikin lumana, haka kuma za ta ci gaba da goyon bayan aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, kana za ta ci gaba da yin kokari domin gina kyakkyawar makomar bil Adam, tare kuma da ciyar da sha'anin shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a fadin duniya gaba yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China