Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in WIPO: Sin na cike da kuzarin kirkire-kirkire
2020-09-19 16:08:53        cri

A kwanakin baya ne babban jami'in hukumar kiyaye ikon mallakar fasaha ta duniya wato WIPO Francis Gurry, ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, ba ma kawai kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ta hukumarsa ba ce, har ma tana goyon bayan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, kana kasar Sin babbar kasuwa ce mai matukar muhimmiya, wadda ta kasance kasar da ta gabatar da rokon neman ikon mallakar fasaha mafi yawa a fadin duniya a cikin shekarar 2019 da ta gabata, har ta kai matsayi na uku wajen gabatar da bukatar neman iznin samun lambar shaidar mallakar fasaha a duniya.

A farkon watan da muke ciki, hukumar WIPO ta fitar da rahoton alkaluman kirkire-kirkiren duniya na shekarar 2020, inda aka bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta kai sahun gaba a fannin, kuma rukunonin kimiyya da fasaha da yawansu ya kai 17 na kasar sun shiga manyan rukunonin kimiyya da fasaha 100 wadanda suka fi rinjaye a duniya, wato kasar Sin ta kai matsayi na biyu bayan Amurka.

Babban jami'in ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne, domin har kullum kasar Sin tana maida hankali kan aikin ingiza ci gaban kirkire-kirkire a kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China