Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta shirya tantance muradun ci gaba mai dorewa a karo na farko
2020-09-19 16:12:56        cri

A jiya Jumma'a MDD ta shirya aikin tantance muradun neman ci gaba mai dorewa a karo na farko, domin duba ayyukan da aka kammala yayin da kasashen duniya suke kokarin neman samun dauwamammen ci gaba, inda babban sakataren MDDr Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashe daban daban da su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cikar burinsu.

Babban sakataren ya bayyana cewa, matakan da kasashen duniya za su dauka a cikin 'yan watanni masu zuwa ko 'yan shekaru masu zuwa, za su haifar da babban tasiri ga muradun ci gaba na MDD nan da shekarar 2030, shi ya sa ya dace a dauki matakan da suka dace domin biyan bukatun ci gaban duniya.

Guterres ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, kasashe masu tasowa suna fuskantar kalubaloli guda biyu, wato batun dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da kuma gujewa rikicin bashi, idan ana son cimma burin samun ci gaba mai dorewa, ya zama wajibi a daidaita matsalolin, tare kuma da daidaita kalubalen tattara kudi cikin matsaikacin lokaci da kuma dogon lokaci, ya kara da cewa, shirin farfadowar tattalin arziki bayan barkewar annobar COVID-19 zai kyautata tsarin tattalin arzikin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China