Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Na'urar binciken duniyar Mars ta Sin ta yi tafiyar kilomita miliyan 155
2020-09-19 16:22:23        cri

Babban mai tsara shirin aikin binciken duniyar Mars na farko na kasar Sin, Zhang Rongqiao, ya ce na'urar binciken duniyar Mars ta Sin samfurin Tianwen-1 ta riga ta yi tafiyar kilomita miliyan 155.

Ya zuwa karfe 8:30 na safiyar Juma'a, na'urar tana cikin yanayi mai kyau a nisan kilomita sama da miliyan 18 daga duniyar mu, Zhang ya bayyana hakan a taron da aka shirya kan ayyukan binciken sararin samaniyar kasar Sin na shekarar 2020 da ake gudanarwa a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian dake gabashin kasar Sin.

Na'urar ta yi nasarar daukar hotunan duniyar da muke ciki da duniyar wata, kuma ta yi nasarar kammala kashin farko na ayyukan binciken da take gudanarwa a sararin samaniyar a tafiyar mai dogon zango, in ji Zhang.

A ranar 23 ga watan Yuli, kasar Sin ta harba na'urar binciken duniyar Mars, wanda ya kasance aiki mai zaman kansa da kasar ta gudanar karkashin shirinta na binciken sararin samaniya. Ana sa ran na'urar za ta isa duniyar Mars mai launin ja ya zuwa watan Fabrairun shekarar 2021.

Ana tsammanin na'urar za ta sauka a watan Mayun shekarar 2021, wato kimanin watanni uku ke nan bayan na'urar Tianwen-1 ta isa zuwa duniyar Mars.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China