Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gaskiya tushen magana ne
2020-09-20 20:38:48        cri

Kwanan nan, jaridar "This Day" da ake wallafawa a Najeriya, ta wallafa wani bayani, dangane da tattaunawar da aka yi da Mukadasshin shugaban cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya, Dr. Efem Ubi, da kuma shugabar kungiyar 'yan kasuwan jihar Lagos, Madam Toki Mabogunje, inda dukkansu suka karyata zargin da kungiyar Heritage Foudation ta kasar Amurka ta yi wa kasar Sin a wani rahoton da ta fitar, cewa wai Sin ta sanya wasu na'urorin satar bayanai cikin gine-ginen da ta gina ma gwamnatocin kasashen Afirka.

A cewar Dr. Efem Ubi, wannan zargin da kungiyar Heritage Foudation ta yi ba shi da tushe ko kadan, sabo da kungiyar ita kanta ba ta iya samar da shaidu kan zarginsa, don haka ya kamata kasashen Afirka sun yi watsi da wadannan jita-jita, da masu kyamar ci gaban kasar Sin ke kokarin yada su a duniya, tare da ci gaba da kokarin hadin gwiwa tare da Sin. Dr. Efem Ubi ya kuma shawarci kasashen Afirka da su ci gaba da huldar tattalin arziki da kasar Sin, huldar da a ganinsa ke samar da dimbin nasarori. Ya ce, yawan jarin da kasar Sin ta samar wa Nijeriya a cikin shekaru 20 da suka wuce, ya zarce gaba dayan jarin da kasashen yammaci suka zuba a kasar a cikin shekaru 150 da suka wuce.

A cewarsa, wasu kasashe masu sukuni da dama sun fi sanin fasahar satar bayanai, misali kasar da ta mallaki kamfanin Google, da sauran shafukan sada zumunta da yawa, ita ce kasar da ya kamata kasashen Afirka su kara mai da hankali kan ta, don magance tsunduma cikin tarko.

A nata bangare, Madam Mabogunye ta ce, zargin da kungiyar ta yi a kan mai da shi jita-jita in an yi nazarinsa ta fannin ilmin doka, kuma babu wanda zai dauki jita-jita a matsayin gaskiya. A cewarta, manyan ababen more rayuwa da kamfanonin kasar Sin suka gina sun taimaka matuka wajen raya harkokin zirga-zirga, da kuma kasuwanci a Nijeriya. Ta ce, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta amfana wa Nijeriya wajen bunkasa manyan ababen more rayuwa da za su taimaka ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Abin haka yake, kasancewarsu kasashen da ke kokarin farfado da tattalin arzikinta, ya zama dole Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka su bunkasa manyan ababen more rayuwarta. Faduwa ta zo daidai da zama ke nan yadda kasar Sin take taimakawa wajen gina manyan ababen more rayuwa a Afirka, ciki har da layin dogo na Mombasa - Nairobi, da na Djibouti-Addis Ababa, sai kuma tashar samar da wuta ta Soubre da ke kasar Cote d'Ivoire da bututun man gas na Tanzania da makamantansu. A Nijeriya ma, layin dogo na Abuja-Kaduna da tashoshin filayen jiragen sama da tashoshin ruwa da sauransu da kamfanonin kasar Sin ke ginawa duk sun taimaka ga ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma a kasar. Har ma shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari a wata sanarwar da aka fitar bayan ganawarsa da babban darektan kamfanin CRCC na kasar Sin Mr. Chen Fenjian a bara, ya bayyana godiyarsa ga kokarin da kasar Sin ta yi wajen inganta manyan ababen more rayuwa a kasarsa. Ya ce, lalacewar manyan ababen more rayuwa a Nijeriya ta haifar da illoli ga rayuwar al'umma, har da mutuwar wasu ko jikkatarsu. Ya ce, kasar Sin ta ba mu sahihin taimako a wajen gina manyan ababen more rayuwa, ta kuma kawo mana fasahohi masu inganci." Amma a maganar satar bayanai, Heritage Foudation za ki iya samar mana shaidu?

Jama'a, mene ne ra'ayinku kuma? (Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China