Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Kashi biyu bisa uku na alummar duniya sun shiga tsarin COVAX na samar da allurar rigakafin COVID-19
2020-09-22 11:18:47        cri

Hukumar lafiyar duniya WHO ta bayyana a ranar Litinin, cewar baki daya kasashe 156 dake wakiltar kashi biyu bisa uku na yawan al'ummar duniya sun shiga tsarin COVAX, wato tsari ne na kasa da kasa na hadin gwiwa da hukumar WHO, wanda aka bullo da shi da nufin ba da damar bai daya ga kasashen duniya wajen samun allurar rigakafin annobar COVID-19.

Wannan ya kushi kasashe 64 mafiya karfin tattalin arziki, wadanda suke samar da kudaden rigakafin COVID-19 cutar a kashin kansu, sai kuma kasashe 92 masu karamin karfi da matsakaicin karfi wadanda za su iya bada taimako ga shirin samar da rigakafin ta hanyar shirin na COVAX, wanda cibiyar Gavi dake tara kudaden tallafawa aikin samar rigakafin ga wadannan kasashen ke jagoranta.

Hukumar WHO ta ce, cibiyar shirin COVAX a yanzu za ta fara shirin kulla yarjejeniya da kamfanonin samar da allurar ragakafin domin samar da alluran rigakafin cutar da ake bukata domin kawo karshen mataki mafi muni na annobar nan da karshen shekarar 2021.

Yayin da duniya ke tsaka da fuskantar annobar COVID-19, kasashen duniya da dama, da suka hada da Jamus, Birtaniya, Sin, Rasha, Faransa da Amurka, suna ta kokarin samar da rigakafin annobar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China