Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta inganta sabon tsarin sayayya bisa ga sabon tsarin kasuwanci
2020-09-22 11:22:19        cri

Babban ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar ba da shawara kan inganta sabon tsarin yin sayayya wanda ya dace da sabon tsarin kasuwanci na zamani.

Takardar ta nuna cewa, za a dauki karin matakan aiwatar da dabarun fadada biyan bukatun kasuwannin cikin gida, da kara fadada girman kasuwannin, da inganta su, bisa ga sabon tsarin sayayya wanda ya dace da sabon tsarin kasuwanci, da kuma bunkasa sabon tsarin ciniki tare da mayar da hankali kan bukatun kasuwannin cikin gida a matsayin jigo, sannan za a baiwa kasuwannin cikin gidan da kuma na ketare damammakin samun bunkasuwa.

Takardar ta ce, bayan shafe shekaru uku zuwa biyar tana ci gaba da yin kokari, kasar Sin za ta inganta dabarunta da manufofinta wajen bunkasa ci gaban sabbin hanyoyin yin sayayya.

Ya zuwa shekarar 2025, kasar Sin za ta kara sabbin biranen kasuwanci da manyan kamfanoni, domin aiwatar da sabon tsarin sayayya, da kara fadada kasuwannin cinikayyar kayayyaki na zahiri ta hanyar intanet, da kuma bunkasa sabon tsarin sayayya, kamar tsarin kasuwanci na ayyukan hidima na zamani wato Internet Plus services.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China