Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya ba MDD
2020-09-22 16:57:57        cri

A jiya Litinin, an yi bikin tunawa da cika shekaru 75 da kafuwar MDD, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ba da shawarwari guda hudu ga Majalisar, don ta kara taka rawar gani a kokarin daidaita al'amuran duniyarmu, wadanda suka kunshi:

 

Tabbatar da adalci a duniya, inda dukkan kasashe, baba ko karama, za su girmama juna, da zama cikin daidaituwa.

Da tsayawa kan kundin MDD da manufofi masu alaka da kundin wajen daidaita huldar kasa da kasa.

Gami da kokarin inganta hadin gwiwar kasa da kasa.

Sa'an nan yayin da ake daukaka ra'ayi na kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban a duniya, ya kamata a yi kokarin daukar matakai, maimakon yin magana fatar baki.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China