Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Wenbin: Akwai karfin gwiwar gudanar da gasar Olympics ta birnin Beijing cikin nasara
2020-09-22 19:38:12        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce yana da karfin gwiwar ganin Sin ta gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturun shekarar 2022 mai kayatarwa. Jami'in ya ce a wannan lokaci da ya rage kwanaki 500 a bude gasar, Sin za ta yi aiki tare da daukacin sassa, don tabbatar da nasarar gasar, wadda ake fatan ta zamo mai ban sha'awa, ta musamman, kuma wadda za ta sha banban da saura.

Wasu rahotanni sun rawaito shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa Thomas Bach na cewa, a wannan gaba da ya rage kwanaki 500 a bude gasar ta birnin Beijing, yana cike da fatan ganin yadda birnin Beijing zai karbi bakuncin gasa mai cike da tarihi.

Game da wannan, Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labarai na Talatar nan, cewar ma'aikatar wajen Sin ta cimma manyan nasarori a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Jami'in ya ce, kwamitin shirya wannan gasa na aiki tare da sauran kwamitocin kasa da kasa masu ruwa da tsaki, don tabbatar da dakile tasirin annobar. An kuma gudanar da jerin shirye-shirye cikin nasara bisa tsari, wadanda suka samu karbuwa daga bangarori na kasa da kasa, ciki hadda babban kwamitin shirya gasar ta Olympics na kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China