Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban CMG: A karfafa hadin gwiwar sassan duniya don kokarin dakile cutar COVID-19
2020-09-22 19:48:54        cri

Wata kungiyar hadin gwiwar kasa da kasa ta fannin aikin telabijin mai alaka da hanyar siliki, da wani reshen kamfani dake karkashin babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya kafa, ta kaddamar da jerin tarukan kasa da kasa, na tattauna batun karfafa hadin gwiwa don tabbatar da wata hanyar siliki mai lafiya, tun daga watan Afrilun bana.

Daga bisani, mataimakin darektan sashi mai kula da aikin fadakarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban rukunin CMG, mista Shen Haixiong, ya rubuta wani bayani domin wannan taro na musamman.

Cikin bayaninsa, mista Shen ya ce kasar Sin ta yi kokarin matuka wajen dakile cutar COVID-19, inda ta zama babbar kasa ta farko da ta fara samun farfadowar tattalin arziki, bayan barkewar annobar. Kana kasar ta yi hadin gwiwa da kasashe daban daban, da ba su fasahohin da ta samu, gami da tallafin kudi da kayayyaki, da zummar ganin bayan cutar a doron kasa.

Mista Shen ya ce, don tattara fasahohi na bangarori daban daban, rukunin CMG ya kaddamar da bikin nan na "shimfida wata hanyar siliki mai lafiya" a watan Afrilu, inda aka samu halartar wasu kwararrun da suka zo daga kasashen Italiya, da Japan, da Argentina, da Amurka , da kuma kasar Sin. Wadanda su ma sun rubuta bayanai don fadakar da al'ummun duniya.

Ban da wannan kuma, mista Shen ya ambaci yadda kungiyar nan ta hadin gwiwar kasa da kasa a fannin aikin telabijin ta yi kokarin hadin kai tare da takwararta ta nahiyar Asiya, da ta kasashen Larabawa, don watsa labarai dangane da yadda ake kokarin dakile cutar COVID-19 a kasar Sin, tare da raba nagartattun fasahohin da kasar Sin ta samu a wannan fanni ga kasashe daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China