Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakaki: Shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar sun samu yabo sosai
2020-09-22 19:49:56        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a yayin taron cika shekaru 75 da kafuwar MDD, ya kunshi shawarwari guda 4, dangane da rawar da ya kamata Majalisar ta taka, bayan da cimma nasarar dakile cutar COVID-19, wadanda suka samu yabo sosai daga bangarorin duniya daban daban.

Mista Wang ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cewa shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar, sun nuna ra'ayin kasar Sin na tsayawa kan tsarin kasa da kasa, a karkashin jagorancin MDD, da kare dokokin kasa da kasa, da rufa ma MDD baya, wajen ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin daidaita al'amuran kasa da kasa, da aiwatar da manufar kasancewar bangarori daban daban masu fada a ji a duniyarmu, gami da kokarin shiga a dama da ita a aikin gyaran fuskar tsarin kula da harkokin kasa da kasa, da yunkurin kafa wata al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China