Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Ya dace a martaba hanyoyin ci gaban da kasashe daban daban suka zaba
2020-09-23 09:39:28        cri

A jiya Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi yayin taron muhawara na babban taron MDD karo na 75, inda ya jaddada cewa, ba zai yiyu ba wata kasa ta samu moriya daga matsalar da sauran kasashe suke fama, kuma ba zai yiyu ba wata kasa ta samu kwanciyar hankali daga tumbuke wasu kasashe, don haka ya dace a nace kan manufar kafa dunkulalliyar duniya domin samun moriya tare ta hanyar gudanar da hadin gwiwa, kana a yi watsi da cacar baka kan bambancin tunani tare kuma da kawar da bambancin wayewar kai, kana abun da ya fi muhimmanci shi ne, a martaba hanyoyin samun ci gaban da kasashen daban daban suka zaba, ta yadda za a ciyar da zamantakewar al'ummun bil Adam ta hanyoyi daban daban da suka dace.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China