Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Bai kamata duniya ta koma zaman 'yan marina ba
2020-09-23 10:35:00        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, tattalin arzikin duniya, ya riga ya dunkule waje guda, kuma juya kai ko nuna halin ko'in kula a wannan fanni ya sabawa dokoki na tarihi.

Xi wanda ya bayyana haka, a jawabin da ya gabatar yayin babban taron MDD karo na 75, ya ce, babu wata kasa a duniya da za ta ware kanta daga dangi. Haka kuma ba za mu iya gudu daga kalubalolin da dunkulewar tattalin arzikin duniya ke kawowa ba, a don haka, kamata ya yi a tuntari manyan kalubaloli, kamar gibin dake tsakanin matalauta da masu wadata da gibin bunkasuwa tsakanin kasashe daban-daban da sauran matsaloli. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China