Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar raya shaanin ilimi, aladu, lafiya da wasanni
2020-09-23 13:42:44        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin raya sassa na ilimi, da al'adu, da lafiya da kuma wasanni.

Shugaban ya bayyana cewa, wadannan sassa na da matukar tasiri a fannin karfafa gamsuwar rayuwa, da samar da farin ciki da tsaro.

Xi ya yi wannan kira ne jiya Talata, yayin taron karawa juna sani da ya jagoranta, taron da ya samu halartar wakilai daga wadannan sassa, domin jin ra'ayinsu game da shirin tsara dabarun ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14, wanda kasar ta Sin za ta aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.

Xi ya kuma bayyana cewa, jam'iyya da gwmnati, suna dora muhammanci matuka, kan sha'anin raya ilimi, al'adu, da lafiya da kuma wasanni, kuma tun taron wakilan jama'a karo na 18 da aka gudanar a shekarar 2012 zuwa wannan lokaci ake daukar jerin matakai.

Ya kara da cewa, ya kamata kwamitocin jam'iyya da gwamnatoci a matakai daban-daban, su fito da shirye-shirye da matakai, don taimakawa sabbin jini taka rawa a shirin farfadowa da kasa da kara samar da sabbin jini da cimma sabbin nasarori a sassa rayuwa daban-daban.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China