Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yaba da jawabin da shugaban kasar Sin ya gabatar a babban taron MDD karo na 75
2020-09-23 13:44:35        cri

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a babbar muhawarar babban taron MDD karo na 75, inda bangarori daban-daban suka amince da matsayin da Xi ya bayyana cikin jawabinsa, a ganinsu, shawarwarin da ya gabatar, sun zayyana alkiblar aikin raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya da raya makomar duniya nan gaba.

Shehun malamin cibiyar nazarin mu'ammalar al'adu da tattalin arzikin dake tsakanin Sin da Afrika ta kasar Zimbabwe Donald Rushambwa ya nuna yabo matuka ga kalaman da Xi ya fadi game da kara hadin kan duniya. A cewarsa, hanya daya tilo da za a bi wajen yakar cutar COVID-19 ita ce hadin kai da taimakawa juna. Sin ta baiwa sauran kasashen taimaka da samar da tallafin kayayyaki, da kuma da more fasaha da dabarun yakar cutar, a don haka, ya zama abin koyi, hakan ya kara muhimmiyar rawa ga wannan yaki da duniya ke yi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China