Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi watsi da zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin
2020-09-23 19:21:26        cri
Wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya kira wani taron manema labaru a jiya Talata, inda ya yi watsi da zarge-zargen da shugaban Amurka ya yi wa kasar Sin. Mr. Zhang ya ce a lokacin da yake jawabi, yayin babban taron MDD, shugaban na Amurka ya zayyana wasu laifuka wadanda Sin ba ta taba aikatawa ba, kuma ba za a taba amincewa da su ba.

A cewar Zhang, a wannan lokacin da ake tsananin bukatar hadin gwiwa a duniyarmu, kasar Amurka tana neman tada zaune-tsaye, da janyo rarrabuwar kawuna. Ya ce, albarkacin sadaukarwa, da kokarin aiki da al'ummar kasar Sin suka yi, kasar ta samu shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri, tare da samar da gudunmawa ga yunkurin dakile cutar a duniya.

To sai dai kuma a hannu guda, kasar Amurka, ko da yake tana da fasahohin jinya mafi cigaba a duniya, da tsarin aikin likitanci mafi inganci, a yanzu ta zama kasar da aka fi samun masu kamuwa da cutar COVID-19, da mutanen da suka rasa rayuka sakamakon cutar.

Zhang ya kara da cewa, yadda kasar Amurka ke daukar mataki na kashin kai, da musgunawa sauran kasashe, ba zai ba ta damar daidaita al'amura ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China