Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Wasu abubuwan da annobar COVID-19 ta nuna mana
2020-09-23 19:28:18        cri

Yayin da yake gabatar da jawabi jiya a wajen taron muhawara na MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zayyana wasu abubuwan da annobar COVID-19 ta nuna ma al'ummar duniya.

A cewarsa, wadannan abubuwa su ne:

Na farko, a wannan zamani, duniyar da muke zama a ciki tamkar wani kauye ne, inda kasashe daban daban suke hadin kai, da cudanya da juna, wadanda suke da makomar bai daya.

Na biyu, tattalin arzikin duniya na ci gaba da dunkulewa waje guda, kana tsarin yana ci gaba da samun karbuwa sosai.

 

Na uku, dan Adam na bukatar gyare-gyare, don kara kokarin karkata ga manufar raya kasa, da salon zaman rayuwa, irin na kare muhalli.

Na hudu, akwai bukatar a hanzarta daidaita tsarin yadda ake kula da al'amuran kasa da kasa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China