Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkawarin da kasar Sin ta yi ya shaida niyyar kasar ta kare muhallin duniya
2020-09-28 14:44:45        cri

A yayin babban taron MDD karo na 75, kasar Sin ta yi alkawarin rage yawan iska mai dumama yanayin da take fitarwa tun daga shekarar 2030, sa'an nan zuwa shekarar 2060, isassun itatuwa da ciyayi da za a dasa a kasar, za su iya shanye dukkan iska mai dumama yanayin da kasar ke fitarwa.

He Jiankun, shi ne mataimakin darektan kwamitin kwararru masu kula da batun sauyin yanayi na kasar Sin, wanda ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin ta sanya wannan buri a fannin rage fitar da iska mai gurbata muhalli ne, don sauke nauyinta a fannin kare muhallin duniya, bisa matsayinta na wata babbar kasa. Mista He ya ce,

"Matakin da muka dauka yana da karfi sosai. Mun kebe wasu shekaru 30 kacal, don farawa daga rage fitar da iska mai dumama yanayi, har zuwa lokacin da za mu kawar da dukkan irin wannan iska da muke fitarwa. Ma iya cewa, saurin da za mu samu, a fannin daidaita tsarin tattalin arziki, da na yin amfani da makamashi, da fannin rage fitar da iska mai dumama yanayi, zai wuce yadda ake gudanar da wadannan ayyuka a wasu kasashe masu sukuni. Ta wannan hanya, mun taimakawa karfafa zukatan al'ummun kasashe daban daban, a kokarinsu na tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya."

A nashi bangare, Xu Huaqing, darektan cibiyar nazarin manyan tsare-tsaren tinkarar sauyin yanayi, da ta hadin gwiwar kasa da kasa a wannan fanni, ya ce sabon alkawarin da kasar Sin ta yi, zai janyo kabulale, gami da damammaki. Wanda zai tilastawa kasar ta Sin sauya fasalinta a fannonin tattalin ariziki da zamantakewar al'umma, don neman samun wani ci gaba mai inganci. Daga bisani, za a samu alfanu sosai, ta fuskar karfin tattalin arziki, da ci gaban al'umma, da kare muhalli, da dai makamantansu. Xu ya ce,

"Alkawarin da muka sanya gaba, zai tilasta mana kara kokarin daidaita tsare-tsarenmu masu nasaba da tattalin arziki, da masana'antu, da makamashi. Za mu iya gaggauta kafa wani tsarin amfani da makamashi mai tsabta, da fitar da iskar dumama yanayi kadan, wanda ke da tsaro da inganci. Haka kuma, za mu takaita yin amfani da kwal a matsayin makamashi, da raya wasu sabbin makamashi na zamani. Duk wadannan matakai za su sanya mu kyautata fasahohinmu, a fannin samar da kayayyaki."

Ban da wannan kuma, yunkuri na ragewa, da kawar da iskar dumama yanayin da ake fitarwa a kasar Sin nan da shekarar 2060, na bukatar samun wani hadin gwiwa tsakanin bangarorin tattalin arziki, da makamashi, da fasahohi. Dangane da wannan aiki, He Jiankun, mataimakin darektan kwamitin kwararru masu nazarin batun sauyawar yanayi, ya ba da shawarar daidaita wasu fannoni. Ya ce,

"Da farko za mu kara kokarin daidaita tsarin tattalin arzikinmu, inda za mu raya wasu sabbin sana'o'i masu nasaba da fasahohi na zamani, saboda wadannan fasahohin za su taimaka wajen rage fitar da iska mai dumama yanayi. Na biyu, za mu yi iyakacin kokarinmu wajen tsimin makamashi, da raya tsarin tattalin arziki na bola jari. Sa'an nan na uku, za mu kara yin amfani da sabbin makamashi, don maye gurbin tsohon makamashi mai gurbata muhalli. A mataki na hudu kuma, a lokacin da muke gudanar da ayyuka masu alaka da aikin gona, da aiki na kula da itatuwa, da dai sauransu, dole ne mu mai da hankali kan aikin kare muhalli, da tabbatar da samun dimbin nau'ikan dabbobi, da itatuwa da ciyayi, don samun ci gaba mai dorewa. Haka kuma, na biyar, za mu kirkiro sabbin fasahohi na ci gaba, da yin amfani da su a cikin masana'antu."

Alkaluman da ma'aikatar muhallin kasar Sin ta samu sun nuna cewa, kasar Sin ta riga ta samar da gudunmowa sosai, ga aikin rage saurin karuwar iska mai dumama yanayi a duniya. Kuma yawan iska mai dumama yanayin da take fitarwa a shekarar 2019, ta ragu da kashi 18.2%, idan an kwatanta jimilar da aka samu a shekarar 2015. Sa'an nan yawan itatuwa da ake da su a kasar su ma sun karu sosai, inda Sin din ta zama kasa da aka fi samun karuwar daji a duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China