Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaruman jamhuriyar kasar Sin da shugaban kasar ya yabawa
2020-10-05 18:06:35        cri

Idan aka waiwayi ci gaban sabuwar kasar Sin cikin shekaru 71 da suka gabata, jarumai maza da mata masu dimbin yawa sun sadaukar da rayukansu kuma suna ci gaba da gwagwarmaya, domin ci gaban kasar da kuma al'ummarta. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha yaba wa jaruman a lokuta daban-daban tare da yin kira ga jama'a da su tuna da dukkan jaruman da suka ba da gudummawa ga kasar, tare da girmamawa da karewa da kuma yi koyi da su.

Barkewar annobar numfashi ta COVID-19 a shekarar 2020, ta sake kawo malam Zhong Nanshan cikin idannun mutane. Shekaru 17 ke nan da suka gabata, har yanzu malamin da ke da shekaru sama da 80 a duniya yana ta fafatawa a gaba-gaba, wajen ceton mutane kamar yadda ya yi a lokacin yaki da cutar SARS a shekarar 2003. A ranar 8 ga watan Satumba, a yayin taron kasa na yabawa aikin yaki da annobar COVID-19, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba Zhong Nanshan babbar lambar girmamawa ta kasa, saboda gaggarumar gudummawar da ya bayar wajen kandagarki da takaita yaduwar cutar SARS da ta COVID-19.

 

 

Bayan karbar lambar yabon, Zhong Nanshan ya ce, "A ganina, ba ni irin wannan girmamawar, kwarin gwiwa ne ga daukacin ma'aikatan kiwon lafiya, da yawa daga cikinsu suna gudanar da ayyuka fiye da yadda muke yi. Ban da wannan kuma, za mu kara daukar nauyi mai girma, don zurfafa ayyukan kandagarki da shawo kan cututtuka a kasarmu."

Tun daga lokacin da aka fara yaki da cutar a farkon shekarar da muke ciki, miliyoyin ma'aikatan kiwon lafiya a duk fadin kasar, suna kokarin ceton rayukan mutane, kuma kusan rabi daga cikinsu matasa ne. Wadannan yara a idannun iyaye, sun girma cikin dare daya, har ma sun zama kashin bayan jamhuriyar kasar Sin a sabon zamani. Xi Jinping ya ce,

"Babu jaruman da suka fado daga sama, sai dai mutanen da suka yi jarumta. Matasa ba sa jin tsoron wahalhalu, matsaloli, da sadaukarwa, suna sauke babban nauyi, da su makomar al'ummar Sinawa ce! Bari mu yaba musu!"

 

 

Tun daga watan Yunin bana, ake ta ruwan sama mai karfi a yankuna da dama na kasar Sin, kuma sama da koguna 800 a larduna 26 sun fuskanci hadarin ambaliyar ruwa, inda suka zarce layin gargadi. Wannan ne halin ambaliyar ruwa mafi muni da aka samu a kasar tun bayan shekarar 1998. Sojoji da jama'a a wurare daban daban sun shiga aikin yaki da ambaliyar ruwa da ceton rayuka don kare yankunansu. A ranar 19 ga watan Agusta, Xi Jinping ya yi tafiya ta musamman zuwa madatsar ruwa ta tabkin Chaohu da ke birnin Hefei na lardin Anhui don ganin halin ambaliya da ake ciki da kuma gaida ma'aikatan yaki da ambaliyar. Inda ya ce,

"Ina so in mika gaisuwa cikin sahihiyar zuciya ga dukkan ma'aikatan da ke yaki da ambaliyar ruwa a duk fadin kasa."

Xi ya kara da cewa, jami'ai da talakawa, da sojoji, sun nuna halinsu na rashin tsoron wahala, gajiya, da sadaukarwa, sun kuma nuna yadda al'ummar kasar Sin ke hadin gwiwa, da taimako da kaunar juna. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China