Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kasashe na sa ran inganta hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin yaki da cutar COVID-19
2020-10-09 14:57:41        cri

Yayin da ake yaki da cutar numfashi ta COVID-19, har kullum kasar Sin na hadin gwiwa sosai tare da kasashen duniya, a kokarin haye wahalhalu tare. Wasu kasashe na ganin cewa, kalaman kasar Sin, da ma abubuwan da take yi, sun shaida yadda kasar ke sauke nauyin dake wuyanta, a matsayinta na kasa mai girma. A waje daya kuma, sun bayyana fatansu, na inganta hadin kai tare da Sin a nan gaba.

Ministar watsa labarai ta kasar Zimbabwe Monica Mutsvangwa ta zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a kwanan baya, inda ta furta cewa, yayin da kasar Sin ke kokarin shawo kan cutar COVID-19 a yankunanta, a gefe guda kuma, tana yin iyakacin kokarinta wajen samar da taimako ga kasarta, da ma sauran kasashe, don haka ta nuna wa Sin matukar godiya. Madam Monica tana mai cewa,

"Tun bayan bullar cutar COVID-19, sau da yawa gwamnatin kasar Sin, da kungiyoyin al'ummarta, sun bai wa Zimbabwe tallafin kayayyaki, har ma ofishin jakadancin kasar Sin da ke Zimbabwen, ya samar da kayayyakin rigakafi a duk mako, lamarin da ya kyautata aikin kandagarki sosai ga ma'aikatan jinya. Ban da haka, gwamnatinmu da ma al'ummarmu, na nuna godiya sosai ga yadda gwamnatin Sin ta turo mana tawagar kwararru masu ilmin likitanci, wadanda suka koya mana fasahohin shawo kan cutar ba tare da boye komai ba, lamarin da ya taimaka mana sosai wajen tinkarar cutar."

A nasa bangaren kuma, wani masanin ilmin harkokin kasa da kasa na kasar Uzbekistan Farkhod Tolipov, ya yi tsokacin cewa, yayin da duk duniya ke yaki da cutar COVID-19, Sin ta nuna yadda take sauke nauyi dake wuyanta, a matsayinta ta kasa mai girma. Ya kara da cewa,

"Yayin da Sin ke fama da cutar COVID-19, ta samar wa kasashe da dama taimako da ma goyon baya don yaki da cutar, ciki har da tallafin jinya, kayayyakin jin kai da dai sauransu. Abin da ya kamata a lura shi ne, wata tawagar kwararrun aikin likitanci ta zo kasarmu, don taimaka wa ma'aikatan jinyar mu a fannin takaita cutar."

Ya zuwa yanzu ma dai, gwamnatin kasar Sin ta riga ta bai wa kungiyar tarayyar Afirka, da ma kasashen Afirka kayayyakin yaki da cutar COVID-19 sau da dama, inda bangarorin Sin da Afirka suka riga suka hada kansu, wajen sufurin kayayyakin zuwa ga kasashen Afirka 20 da ba sa kusa da bakin teku.

Bisa kididdigar da aka fitar, an ce, Sin ta riga ta tura tawagogin kwararru zuwa kasashen Afirka 13, don ba da taimako bisa bukatun kasashen da abin ya shafa. Kadara Swaleh, shugaba ne dake kula da harkokin siyasa a Jam'iyyar Jubilee mai mulkin kasar Kenya, ya kuma furta cewa,

"Kasar Sin ta samar wa duniya taimako a fannonin fasahohi, da kayayyakin rigakafi da dai sauransu. Muna gode mata sosai. Yadda ta koya mana fasahohin yaki da cutar COVID-19 da ma samarwa duniya kayayyakin kandagarki ya burge ni sosai. Wani karin magana a harshen Siwahili na nuna cewa, "ko a gaban babban bala'i daga Indallahi, tabbas za a samu mafita". Abin da muke gani shi ne, yadda kasar Sin ta hada kai tare da duniya, da ma tallafa wa duniya, ba tare da kawo baraka ga duniya ko kadan ba, yayin da ake yaki da annobar."

Bugu da kari, Mr. Swaleh ya yi tsokacin cewa, yana fatan inganta hadin kai tare da kasar Sin a nan gaba.

"Ko batun allurar rigakafi, ko na farfado da tattalin arziki, dukkansu na bukatar hadin kan kasashen duniya, a kokarin samun mafita. A matsayina na dan kasar Kenya kana dan Afirka, ina da imanin cewa, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa a zamanin bayan shawo kan annobar. Muna bukatar kasar Sin, muna bukatar dabarun Sin na farfado da duniya."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China