Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da allurar rigakafin annobar COVID-19
2020-10-16 09:36:26        cri


Jakadun kasashen nahiyar Afirka da ke aiki a kasar Sin da wakilan wasu cibiyoyin Afirka a kasar Sin 51, sun ziyarci babbar cibiyar gwaje gwaje da binciken rigakafin cututtuka ta kamfanin Sinopharm CNGB na Sin.

An bayyana ziyarar jami'an a matsayin wata dama ta zurfafa hadin gwiwa a fannin yaki da cutar COVID-19, tare da gina managarcin tsarin kiwon lafiya tsakanin al'ummun Sin da na nahiyar Afirka.

Kaza lika jami'an jakadancin sun ganewa idanun su, kayan bincike da aka baje a cibiyar, da ma dajin gwaji na zamani, kana sun samu karin haske game da matakan baya bayan nan na gwajin rigakafin cutar COVID-19 da cibiyar kamfanin ke gudanarwa.

Wannan ne dai karo na farko da sakatariyar kwamitin bibiya game da ayyukan dandalin FOCAC, ya shirya wani aiki a zahiri, tun bayan barkewar cutar COVID-19.

Cibiyar Sinopharm CNGB ce irin ta mafi girma a kasar Sin, kuma ta 5 a duniya baki daya, a fannin gwaje gwaje da bincike da samar da rigakafi. Wakiliyarmu Kande ta samu damar yin hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da ziyararsa a cibiyar da dai sauransu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China